Democrat Ta Jero Abubuwan da za Ta Bincika kan Trump bayan Cin Zabe

Democrat Ta Jero Abubuwan da za Ta Bincika kan Trump bayan Cin Zabe

  • Jam'iyyar Democrat ta Amurka ta fara shirin ƙalubalantar manufofin Shugaba Donald Trump bayan samun rinjaye a majalisun dokokin ƙasar biyu
  • 'Yan jam'iyyar sun ce za su mayar da hankali wajen rage tsadar rayuwa, matsin tattalin arziki da yaƙin Iran, tare da gudanar da bincike
  • Shugaban 'yan Democrat a Majalisar Wakilai, Hakeem Jeffries ya yi alƙawarin bincikar abin da ya kira cin hanci da rashawa da ba a taɓa ganin irinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Jam'iyyar Democrat ta shirya fara ɗaukar matakan doka da siyasa domin kalubalantar manufofin Shugaba Donald Trump, bayan nasarar da ta samu a zaɓen tsakiyar wa'adin mulki na ranar 3 ga Nuwamba, 2026.

Nasarar ta ba jam'iyyar damar karɓe rinjaye a majalisar wakilai da majalisar dattawa, wanda zai ba ta ikon gudanar da bincike kan gwamnatin Trump, ƙalubalantar manufofinta da sauransu.

Kara karanta wannan

Abdul El Sayed: Musulmi na farko ya lashe zaben sanata a Amurka

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Duk da haka, NBC ta ce har yanzu Trump yana da ikon ƙin amincewa da dokokin da majalisa ta amince da su, yayin da dokokin majalisar dattawa ke ba wa 'yan Republican damar dakatar da wasu ƙudurori.

Aikin da Democrat za ta yi

Shugaban 'yan Democrat a Majalisar Wakilai, Hakeem Jeffries, ya yi alƙawarin gabatar da wasu ƙudurori cikin sa'o'i 100 na farko bayan fara sabon zaman majalisa a watan Janairu.

Abubuwan da jam'iyyar ke son mayar da hankali a kansu sun haɗa da rage tsadar rayuwa, dawo da tallafin inshorar lafiya da wa'adinsa ya ƙare, da kuma soke kusan dala tiriliyan 1 da aka rage daga kasafin shirin Medicaid ƙarƙashin gwamnatin Trump.

Haka kuma, suna son a soke wasu harajin shigo da kayayyaki da gwamnatin Trump ta kakaba tare da matsa lamba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran, wanda ya taimaka wajen ƙara farashin man fetur.

Samun rinjaye a majalisun biyu zai ba Democrat damar gabatar da ƙudurorinsu domin a kaɗa musu ƙuri'a, tare da shiga tattaunawar yadda za a kashe kuɗin gwamnati.

Kara karanta wannan

Obama ya ce za a fara shirin rage 'barnar' Trump bayan kwace ikon majalisa

Jam'iyyar za ta iya amfani da wa'adin amincewa da kasafin kuɗin gwamnati wajen neman Trump ya amince da wasu buƙatunta, duk da cewa takaddama kan kasafin na iya janyo dakatar da ayyukan gwamnati.

Democrat ta shirya binciken Trump

ABC ta wallafa cewa binciken ayyukan gwamnatin Trump na daga cikin abubuwan da Democrat suka fi ba muhimmanci bayan nasarar da suka samu.

Robert Garcia, wanda ake sa ran zai jagoranci kwamitin sa ido na Majalisar Wakilai, ya wallafa saƙo a kafafen sada zumunta ga 'yan Republican da kalmar da ke nufin su nemi lauyoyi domin kare kansu.

Shi ma Sanata Ron Wyden na jihar Oregon ya wallafa kalma guda ɗaya mai nufin takardun sammaci da ake amfani da su wajen tilasta wa mutane gabatar da bayanai ko shaida.

Majalisar Amurka
Zauren majalisar dokokin Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Da ikon da jam'iyyar ta samu a kwamitocin majalisun biyu, za ta iya gayyatar jami'an gwamnati domin amsa tambayoyi, neman takardu da gudanar da zaman sauraron bayanai a bainar jama'a.

Abubuwan da ake sa ran za su shiga binciken sun haɗa da harkokin kasuwanci da kuɗaɗen intanet na iyalan Trump, kwangilolin gwamnati da suka shafi attajirin Elon Musk, rage ma'aikata da hukumomin gwamnati da sauransu.

Kara karanta wannan

Abubuwa sun kwabewa Trump, 'yan Democrat za su samu yadda suke so a majalisa

Haka kuma, Democrat sun nuna sha'awarsu ta binciken yadda gwamnatin Trump ke kula da takardun da suka shafi marigayi Jeffrey Epstein, wanda aka taɓa samu da laifukan lalata da yara.

Maganar da Obama ya yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi martani bayan jam'iyyarsa ta Democrat ta samu nasara a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin ƙasar.

Barrack Obama ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa Amurkawa na son shugabanci da ke haɗa kan jama'a maimakon rarrabasu.

Ya kuma buƙaci 'yan jam'iyyarsa su mayar da hankali wajen kawo sauye-sauye da rage illolin manufofin gwamnatin Trump cikin shekaru biyu da suka rage mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng