Abdul El Sayed: Musulmi na Farko Ya Lashe Zaben Sanata a Amurka
- Abdul El-Sayed, ɗan jam'iyyar Democrat, ya lashe zaɓen sanatan Amurka a jihar Michigan bayan doke ɗan takarar Republican, Mike Rogers
- Rahotanni sun nuna cewa nasarar El-Sayed ta sanya shi zama Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin sanata a tarihin Amurka
- Zaɓen ya kasance cikin waɗanda suka fi ɗaukar hankali a zaɓen tsakiyar wa'adi na 2026, inda Democrat suka samu rinjaye a majalisun dokokin Amurka biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Michigan, Amurka – Abdul El-Sayed, tsohon daraktan kula da lafiyar jama'a na gundumar Wayne, ya lashe zaɓen sanatan Amurka a jihar Michigan.
El-Sayed ya doke Mike Rogers, tsohon ɗan majalisar wakilan Amurka kuma ɗan jam'iyyar Republican, a zaɓen da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamba, 2026.

Source: Getty Images
Rahoton USA Today ya bayyana cewa nasarar tasa ta zo ne a lokacin da jam'iyyar Democrat ta samu nasarori a zaɓukan ƙasar, tare da karɓe rinjayen kujerun majalisun dokoki biyu.
Abdul El-Sayed ya yi nasara
El-Sayed, wanda aka haifa a jihar Michigan ga iyayensa 'yan gudun hijira daga Masar, ya kafa tarihi a matsayin Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin sanatan Amurka.
Nasarar tasa ta kawo ƙarshen fafatawar siyasa mai zafi tsakaninsa da Rogers, wadda ta kasance ɗaya daga cikin zaɓukan da aka fi mayar da hankali a kansu a zaɓen tsakiyar wa'adi na bana.
A lokacin yaƙin neman zaɓe, 'yan takarar biyu sun sha kai wa juna hare-haren kalamai, inda wasu daga cikin magoya bayan Rogers, ciki har da Shugaba Donald Trump, suka yi amfani da kalaman da aka bayyana a matsayin masu nuna ƙiyayya ga Musulunci wajen yaƙar El-Sayed.

Source: Getty Images
Rikicin cikin gida a Democrat
Zaɓen Michigan ya zama wani fagen fafatawa tsakanin masu ra'ayin sassauci da masu ra'ayin sauyi a cikin jam'iyyar Democrat.
Wasu manyan shugabannin jam'iyyar sun goyi bayan Haley Stevens a zaɓen fitar da gwani, suna ganin ita ce za ta fi samun damar doke Rogers a babban zaɓen.
Sai dai El-Sayed ya doke Stevens a zaɓen fitar da gwani na ranar 4 ga Agusta, lamarin da ya sa wasu 'yan Democrat masu ra'ayin sauyi suka ɗauki nasararsa a Michigan a matsayin wata dama ta nuna cewa 'yan takararsu za su iya yin nasara a sauran jihohi.
A kwanakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe, Rogers ya samu goyon bayan Stevens, wadda ta sha kaye a hannun El-Sayed.
Ilhan Omar ta lashe zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zaɓe a gundumar Minnesota bayan ta doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, John Nagel.
Nasarar ta ba Omar damar ci gaba da wakiltar gundumar da take kai wa tun shekarar 2019, inda za ta fara wa'adi na biyar a majalisar.
Omar, wadda 'yar asalin Somaliya ce kuma ta taɓa zama 'yar gudun hijira, ta samu nasarar ne a daidai lokacin da take fuskantar suka daga Donald Trump.
Asali: Legit.ng

