Gwamnatin Katsina Ta Dauki Mataki kan Sarkin Daura bayan Bullr Bidiyonsa da Baturiya

Gwamnatin Katsina Ta Dauki Mataki kan Sarkin Daura bayan Bullr Bidiyonsa da Baturiya

  • Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin bincike kan zargin cin zarafin wata ’yar yawon buɗe ido daga ƙasar waje da ake yi wa Sarkin Daura
  • Haka zalika gwamnatin ta dauki matakin dakatar da harkokin masarauta da tafiye-tafiyen sarkin har sai an kammala bincike
  • Gwamna Dikko Radda ya ce sakamakon binciken zai jagoranci matakin da gwamnati za ta ɗaukana gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata ’yar yawon buɗe ido daga ƙasar waje da ake yi wa Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar.

Gwamnatin ta kuma sanar da dakatar da halartar harkokin hukuma, aikace-aikace da tafiye-tafiyen basaraken har sai an kammala binciken.

Sarkin Daura.
Mai martaba Sarkin Daura da ke jihar Katsina, Alhaii Faruk Umar Faruk Hoto: Daura Emirtes
Source: Facebook

An bayyana waɗannan matakai ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Dr Bala Salisu Zango, ya fitar a ranar Talata a madadin gwamnatin Katsina kuma kakakin gwamna, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan bidiyon Sarkin Daura da baturiya ke zarginsa

Gwamna Dikko Radda ya dauki mataki

A cewar sanarwar, Gwamna Dikko Umaru Radda ya nuna matuƙar damuwa kan zarge-zargen, yana mai cewa lamarin na buƙatar kulawa ta musamman da ɗaukar matakan da suka dace.

Saboda haka, gwamnan ya bayar da umarnin gaggauta kafa kwamitin bincike domin nazarin zarge-zargen da kuma ba gwamnati shawara kan matakin da ya kamata ta ɗauka.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne saboda muhimmancin zarge-zargen da kuma buƙatar gano gaskiyar abin da ya faru.

Gwamnatin Katsina ta yi alkawarin adalci

Gwamnatin ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci, tare da bayyana cewa za ta aiwatar da dukkan shawarwari da sakamakon bincike da kwamitin zai gabatar bayan kammala aikinsa.

Ta ce dakatar da harkokin hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin Daura na daga cikin matakan da ta ɗauka yayin da ake ci gaba da binciken lamarin.

Haka kuma, gwamnati ta yi kira ga mazauna jihar Katsina da sauran jama’a da su kwantar da hankulansu, su kiyaye doka da oda, tare da guje wa duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

Dikko Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda a fdar gwamnatinsa Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Source: Facebook

Ta buƙaci mazauna jihar Katsina da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, tana mai jaddada aniyarta ta tafiyar da lamarin yadda ya kamata.

Ana sa ran sakamakon binciken kwamitin zai zama jagora wajen matakan da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Dikko Radda za ta ɗauka a gaba.

Instagram ta cire bidiyon Sarkin Daura

A wani labarin, kun ji cewa 'yar ƙasar waje da ta zargi Sarkin Daura da ke Jihar Katsina da taɓa jikinta ba tare da izininta ba yayin ziyarar da ta kai fadarsa, ta ce an cire bidiyon abin da ya faru daga shafinta na Instagram.

Matar ta bayyana cewa ta nemi a sake duba matakin da Instagram ya ɗauka na cire bidiyon, inda ta buƙaci a gudanar da bincike domin tantance ko matakin ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262