An Taru don Hada kan 'Yan Adawa a Kifar da Tinubu a Gidan Babban Fasto
- Babban malamin cocin Katolika, Cardinal John Onaiyekan, ya goyi bayan ƙoƙarin jam’iyyun adawa na haɗa kai domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Ƙungiyar G100 ta sanar da cewa za ta gudanar da taronta na biyu a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, inda jam’iyyun za su amince da wasu muhimman takardu kan haɗin kai
- Onaiyekan ya ce haɗin kan ’yan adawa zai taimaka wajen samar da zaɓi na gari ga ’yan Najeriya, tare da jaddada muhimmancin shugabanni masu gaskiya da ƙwarewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Babban malamin cocin Katolika, Cardinal John Onaiyekan, ya nuna goyon bayansa ga ƙoƙarin jam’iyyun adawa na haɗa kai domin gabatar da matsaya guda gabanin babban zaɓen 2027.
Ƙungiyar G100, wadda ta ƙunshi shugabanni da sakatarorin ƙasa na wasu jam’iyyun siyasa, ta gana da malamin addinin a gidansa da ke Abuja ranar Alhamis.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Salihu Lukman ya bayyana cewa shugabannin sun sanar da Onaiyekan matakan da suke ɗauka domin samar da haɗin kan ’yan adawa da kuma gabatar wa ’yan Najeriya da zaɓin shugabanci na gari.
Wadanda suka gana da Onaiyekan
Daga cikin waɗanda suka halarci ganawar akwai shugaban ɓangaren jam’iyyar PDP, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, SAN, da sakataren wannan ɓangaren, Daniel Woyengikuro.
Haka kuma, shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa, Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe, da shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba Ahmed, sun halarci taron tare da sakataren PRP na ƙasa, Sunny Kanu.
Leadership ta wallafa cewa Farfesa Jibrin Ibrahim, masani kuma mai rajin kare muradun al’umma, shi ne ya taimaka wajen shirya ganawar.
Sanarwar ta ce shugabannin sun bayyana wa Onaiyekan irin ƙoƙarin da suke yi na haɗa jam’iyyun adawa domin samar da wata hanya ta siyasa da za ta ba ’yan Najeriya damar samun shugabanci mai inganci.
Shirin hada kan 'yan adawa
Shugabannin ƙungiyar sun sanar da Cardinal Onaiyekan cewa sun kammala aikin tsara muhimman takardu guda uku da za su jagoranci ayyukan haɗin gwiwarsu.
Takardar farko ita ce yarjejeniyar ƙasa domin farfaɗo da dimokuraɗiyya, wadda ta bayyana ƙa’idoji da manufofin ƙungiyar.
Takarda ta biyu ta ƙunshi tsarin haɗin kan ’yan adawa, wanda ya bayyana yadda jam’iyyun za su yi aiki tare, yayin da ta uku ta ƙunshi shirin gyaran ƙasa.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce ƙungiyar na ƙoƙarin kammala waɗannan takardu tare da amincewa da su kafin taronta na biyu da za a gudanar ranar 9 ga Nuwamba, 2026.
A yayin taron, ana sa ran jam’iyyun da ke cikin ƙungiyar za su amince da takardun tare da bayyana su a hukumance.
Bayanin Fasto Onaiyekan
Cardinal Onaiyekan ya bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin jam’iyyun adawa da ’yan takararsu na haɗa kai, yana mai cewa samar da hamayya mai ƙarfi na da muhimmanci wajen dorewar tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ya kuma bayyana farin cikinsa kan yiwuwar ’yan Najeriya samun zaɓuɓɓuka na gari a zaɓen shekara mai zuwa, domin su yanke shawarar irin shugabannin da suke son su jagorance su.
Malamin addinin ya jaddada cewa shugabanni masu ƙwarewa, gaskiya da tausayi suna da muhimmanci wajen magance matsalolin da ke hana jama’a rayuwa cikin walwala.
Atiku ya dawo jakadan TMG
A wani labarin, kun ji cewa mambobin ƙungiyar Tinubu Must Go (TMG) sun gana da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
A cewar Abba Hikima, an karrama Atiku a matsayin babban jakadan TMG, a wani mataki na girmama gudunmawar da mambobin ƙungiyar ke bayarwa wajen yaɗa manufofinta a faɗin ƙasar.
Taron ya samu halartar wasu shugabannin jam’iyyar PDP da kwamitin yaƙin neman zaɓe, ciki har da Rotimi Amaechi, Sanata Austin Akobundu, Abdussamad Ibrahim Dasuki.
Asali: Legit.ng


