Isra'ila Ta Yi wa Trump Kunnen Uwar Shegu, Ta Kaddamar da Sababbin Hare Hare
- Kasar Isra'ila ta kai sababbin hare-haren sama a kudancin Lebanon duk da cewa Shugaba Donald Trump ya yi gargadi a kan irin wannan matakin
- Donald Trump ya gargadi Benjamin Netanyahu da ya nuna taka-tsantsan kan rikici da Lebanon, yana mai cewa an dade ana yakin Hezbollah
- Iran dai ta fito ta gargadi Isra’ila cewa ci gaba da hare-hare ko mamaye yankunan Lebanon zai saba wa sabuwar yarjejeniyar da aka kulla
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lebanon - Isra'ila ta kai sababbin hare-hare a kudancin Lebanon, duk da sukar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi kan matakan da Tel Aviv ke dauka a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Laraba, jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare a yankin Nabatieh al-Fawqa da kuma wajen garin Kfar Tebnit da ke makwabtaka da shi.

Source: Getty Images
Trump ya gargadi Netanyahu kan Hezbollah
Rahoton BBC ya nuna cewa an kai harin ne a wasu wurare da ake zargin mayakan Hezbollah ke amfani da su, ko da yake rundunar sojin Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan sabon harin ba.
A ranar Talata, Donald Trump ya bayyana cewa ya kamata Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya kasance mai taka-tsantsan wajen tafiyar da rikicin Lebanon.
Da yake magana yayin taron kungiyar G7 a Faransa, Trump ya ce:
"Isra'ila ta dade tana fada da Hezbollah, kuma mutane da yawa na ci gaba da rasa rayukansu."
Ya kuma bayyana cewa bai gamsu da wani hari da Isra'ila ta kai a baya ba, yana mai cewa harin ya yi yawa fiye da yadda ya kamata.
Trump ya kara da cewa dangantakarsa da Netanyahu tana da kyau, amma hakan ba ya hana shi bayyana ra'ayinsa idan ya ga wani mataki da bai dace ba.
Hare-hare sun ci gaba duk da yarjejeniyar Iran
Tun bayan sanar da yarjejeniyar sulhu tsakanin Amurka da Iran a daren Lahadi, Isra'ila da Hezbollah suka ci gaba da musayar hare-hare, in ji rahoton Yahoo News.
A ranar Lahadi din, wani hari da Isra'ila ta kai a Beirut bayan harba rokoki daga Lebanon ya kara jefa tattaunawar sulhun cikin wani mummunan yanayi.
Rahotanni sun nuna cewa Pakistan, wadda ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani, ta ce yarjejeniyar da ake kokarin kammalawa ta kunshi batun Lebanon.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi dai ya gargadi cewa kasarsa za ta dauki duk wani sabon hari da Isra'ila za ta kai a Lebanon ko ci gaba da kasancewar sojojinta a yankin a matsayin karya yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma da Amurka.

Source: Getty Images
Ranar rattaba hannu kan yarjejeniyar
Ma'aikatar harkokin wajen Switzerland ta bayyana cewa ana sa ran Amurka da Iran za su rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Juma'a a garin Bürgenstock.
Trump ya ce zai iya gudanar da taron manema labarai domin karanta yarjejeniyar gaba daya ga duniya.
Ya kuma yi ikirarin cewa yarjejeniyar za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya, tare da bude mashigar ruwa ta Hormuz domin harkokin kasuwanci ba tare da wata matsala ba.
Zargin amfani da sinadari mai guba a Lebanon
A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar sojin Isra’ila ta yi amfani da wani sinadari mai guba wanda zai iya yin matuƙar illa a wuraren da jama’a ke zaune a Lebanon.
An ga hayaki na musamman da ke fitowa daga irin wannan makami har zuwa ranar 30 ga Mayun 2026 a Nabatieh, wani birni mai mutane 40,000.
Sauran bidiyoyin da aka tabbatar da sahihancinsu sun nuna cewa an yi amfani da sinadarin a kusa da birnin Tyre da ke bakin teku da wasu garuruwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


