Babbar Magana: Trump Ya Bayyana Zabi 2 da Iran Ke da Su a Yakin da Ake Yi

Babbar Magana: Trump Ya Bayyana Zabi 2 da Iran Ke da Su a Yakin da Ake Yi

  • Shugaban kasar Amukra Donald Trump ya bayyana zabin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da su
  • Donald Trump ya zargi shugabannin Iran da yin magana biyu kan batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu
  • Shugaban na kasar Amurka ya kuma bayyana cewa babu wani abu da zai rika shiga cikin Iran ba tare da amincewarsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran na da zaɓi tsakanin cimma yarjejeniya da Amurka ko miƙa wuya gaba ɗaya.

Trump ya soki Iran kan rashin amincewa da tattaunawa, yana mai cewa hukumomin ƙasar suna ikirarin cewa hulɗarsu ta tsaya ne kan Oman kaɗai.

Trump ya gargadi shugabannin Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta sake tayar da sabon tarnaki bayan ikirarin Trump

Shugaba Trump ya zargi Iran

A sakon da ya wallafa, Trump ya zargi shugabannin Iran da yin magana biyu kan batun tattaunawar.

“Shugabannin Iran suna da yaudara matuƙa! Su ne suka nemi a yi tattaunawa, wasu ma za su ce sun roƙa, aka fara tattaunawa, kuma an shirya ƙarin zama nan ba da jimawa ba, sai kuma suka fito fili cikin alfahari suna cewa ba sa tattaunawa kuma babu wani abu da ake tattaunawa a kai, suna hulɗa da ‘Oman’ kaɗai.”

- Shugaba Donald Trump

Ya ƙara da cewa Iran na ci gaba da bayyana cewa za ta riƙa sarrafa mashigar Hormuz da ƙarfi, duk da ikirarinsa cewa rundunar sojin ruwan Amurka ta riga ta mallaki yankin.

“Daga nan sai su ci gaba da surutansu na yau da kullum suna cewa su ne za su riƙa sarrafa mashigar Hormuz da ƙarfi, alhali rundunar sojin ruwan Amurka ta riga ta mallake ta gaba ɗaya, tare da ‘ƙawancen toshe hanya’ ko kuma abin da wasu ke kira ‘Katangar Ƙarfe ta Amurka’.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Iran ta jawo matsala da Trump ya yi sabuwar barazana

- Shugaba Donald Trump

Barazanar Trump ga Iran

Shugaban Amurka ya ce babu wani abu da zai shiga Iran sai idan Amurka ta amince, yana mai jaddada cewa hakan ba zai canja ba sai an cimma yarjejeniya ko Iran ta miƙa wuya gaba ɗaya.

“Babu wani abu da zai shiga Iran sai idan muna so, kuma babu abin da zai shiga sai an cimma yarjejeniya ko kuma an miƙa wuya gaba ɗaya.”

- Shugaba Donald Trump

Shugaba Trump ya ce ko Iran ta amince ko ba ta amince ba, ana tattauna mafita kan matsalar da ya ce ƙasar ta haddasa tsawon shekaru da dama.

Trump ya kammala da cewa:

“Abin mai sauƙi ne, Iran ba za ta taba samun makamin nukiliya ba!"
Trump ya ragargaji shugabannin Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Amurka na neman dabara kan Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Amurka ta fara neman sababbin dabaru daga jami'anta kan yadda za a kara matsa wa Iran lamba.

Wani babban jami'i a sashen leken asirin rundunar Amurka ta CENTCOM ya bukaci masu nazari su gabatar da sababbin shawarwari kan hanyoyin da za a hukunta Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng