"Dama Ta Karshe": Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Iran

"Dama Ta Karshe": Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Iran

  • Donald Trump ya ce wannan ita ce dama ta karshe da Iran ke da ita na rattaba hannu kan yarjejeniya mai kyau
  • Shugaban Amurka ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Iran tare da goyon bayan Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar
  • Trump ya ce ba zai amince Iran ta sanya kudin wucewa ta Mashigar Hormuz ba wadda ake ta takaddama a kanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce wannan ita ce dama ta karshe da Iran ke da ita na rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai kyau.

Shugaban kasar na Amurka ya sake jaddada cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Trumpp ya yi gargadi ga Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a Oval Ofis Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Trump ya bayyana zabi 2 da Iran ke da su a yakin da ake yi

Trump ya ce Amurka na tattaunawa da Iran

Trump ya ce ana gudanar da tattaunawar ne bisa bukatar Iran, tare da goyon bayan Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Qatar, da kuma wasu kasashe.

“A yanzu muna tattaunawa da Iran bisa bukatar Iran, tare da goyon bayan Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar musamman, da kuma wasu kasashe."
"Kasashe da dama sun kira, amma idan hakan bai faru ba, wannan ita ce damarsu ta karshe ta rattaba hannu kan yarjejeniya mai kyau.”

- Shugaba Donald Trump

Trump ya yi gargadi ga Iran

Trump ya nuna cewa hakurinsa na kara karewa, yana mai cewa wannan ita ce dama ta karshe da Iran ke da ita yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

Tun da farko, ya soki shugabannin Iran a wani sako da ya wallafa a Truth Social, inda ya zarge su da yin ikirarin da ba daidai ba.

Ya ce duk lokacin da ya bayyana cewa ana tattaunawa, ana gudanar da tattaunawar ne, amma daga baya jami’an Iran su kan fito su ce ba haka ba.

Kara karanta wannan

Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta sake tayar da sabon tarnaki bayan ikirarin Trump

Batun mashigar Hormuz

Da aka tambaye shi ko Iran za ta amince a sake bai wa jiragen ruwa damar wucewa cikin ‘yanci a Mashigar Hormuz, Trump ya ce ba zai bari Iran ta sanya kudin wucewa ba.

“Dole ne wucewar ta kasance cikin ‘yanci. Ba zan bari su sanya kudin wucewa ba. Idan wani zai sanya kudin, mu ne za mu sanya saboda mu ne ke da cikakken iko.”

- Shugaba Donald Trump

Trump ya kuma ambaci yiwuwar amfani da wani matakin kulle hanya, amma ya jaddada cewa ba za a sanya kudin wucewa ba.

“Akwai wani abu da ake kira kulle hanya. A’a, a’a, ba za a sanya kudin wucewa ba. Ba ma tattaunawa kan batun sanya kudin. Ba za a sanya wani kudi ba.”

- Shugaba Donald Trump

An mayar da hankali kan Hormuz

Rahotanni sun nuna cewa babban matakin farko da ake son cimmawa ta hanyar tattaunawar shi ne sake bude Mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya

Trump ya ce ya kamata a bude mashigin ranar Talata, lamarin da ya yi kama da sanya wa Iran wa’adin aiwatar da hakan, duk da cewa bai bayyana takamaiman wa’adi ba. Ya ce za a bude mashigar domin kowa ya rika wucewa ba tare da biyan wani kudi ba.

Bayan haka, bangarorin za su koma tattaunawa kan batun kawar da makaman nukiliya daga Iran, wanda Trump ya ce zai dauki lokaci mai tsawo.

Trump ya ja kunnen Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta karyata Trump

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta musanta ikirarin shugaban Amurka, Donald Trump, cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nemi Amurka kada ta sake kai mata sabon hari.

Iran ta yi kalaman ne bayan shugaban kasar na Amurka ya yi ikirarin cewa ya dakatar da hare-haren bayan sun nemi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng