Sulhu tsakanin Iran da Amurka Ya Fusata Isra'ilawa, Sun Dura kan Netanyahu

Sulhu tsakanin Iran da Amurka Ya Fusata Isra'ilawa, Sun Dura kan Netanyahu

  • Isra’ilawa daga bangarori daban-daban sun nuna fushi kan yarjejeniyar farko tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa yan ƙasar suna kallonta a matsayin barazana ga tsaron Isra’ila yayin da ake tsaka da yaki
  • Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce zai ci gaba da hana Iran mallakar makamin nukiliya, ko da yarjejeniya ta tabbata ko ta rushe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Kudurin sulhu na wucin gadi tsakanin Amurka da Iran ya haifar da fushin Isra’ilawa.

An tabbatar da cewa yan kasar daga bangarorin siyasa daban-daban su bayyana yarjejeniyar a matsayin masifa ga Isra’ila.

Isra'ilawa sun dura kan Benjamin Netanyahu
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei, Shugaba Donald Trump na Amurka da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Maimakon dora laifi kan Amurka kawai, da dama sun karkata fushinsu zuwa ga Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, cewar AP News.

Matsayar Netanyahu kan yarjejeniyar Amurka, Iran

Kara karanta wannan

Iran ta fara samun tagomashi daga Turai bayan tsayar da yaki da Amurka

A wani taron manema labarai da aka gudanar, Netanyahu ya ce ko da an cimma yarjejeniya ko ba a cimma ba, zai ci gaba da yaki.

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce hana Iran mallakar makaman nukiliya, duk da cewa Tehran ta dade tana cewa shirinta na nukiliya domin farar hula ne.

Netanyahu ya ce muddin yana rike da mukamin Firayim minista, ba zai bari Iran ta samu irin wadannan makamai ba, domin hakan barazana ce.

Ya kuma bayyana cewa Amurka ce ta kulla yarjejeniyar, ba Isra’ila ba, yana mai cewa bai amince da bukatar Iran ba.

Iran ta bukaci Isra’ila ta janye dakarunta daga Lebanon a matsayin wani bangare na yarjejeniyar, amma Netanyahu ya ce hakan ba faru ba.

Ya ce dagewarsa da tsayawa tsayin daka ne suka hana aiwatar da wannan bukata, yana mai nuna cewa bai sassauta matsayinsa ba.

Yan Isra'ila sun yi fatali da maganar sulhu
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Isra'ilawa na sukar yarjejeniyar da ake yi

Sai dai jami’an gwamnati, abokan adawa, 'yan siyasa da masu sharhi sun yi gaggawar sukar yarjejeniyar da kuma jagorancin Netanyahu.

Wadannan martani daban-daban sun zama tamkar kuri’ar ra’ayin jama’a kan shugabancinsa gabanin zaben da za a gudanar a Isra’ila a kaka mai zuwa.

Kara karanta wannan

Iran da Amurka sun cimma yarjejeniya, farashin mai ya fara sauka kasa

Masu sukar sun ce Benjamin Netanyahu ne ya ja Shugaban Amurka Donald Trump cikin yakin da Iran ta shiga, tare da yin alkawuran da suka wuce kima.

Sun ce Trump na iya fitar da Isra’ila daga rikicin kafin kasar ta ga ta cimma burinta, lamarin da ya jawo damuwa, cewar France24.

Har ila yau, masu sukar sun ce Netanyahu bai tantance yadda Trump ke kallon dogon rikici ba, kuma Iran ta fi shi dabara.

Sun kara da cewa Netanyahu na kara zama saniyar ware a cikin gida, a yankin Gabas ta Tsakiya da ma a dangantakarsa da Amurka.

Trump ya magantu kan matsayarsa da Iran

Mun ba ku labari a baya cewa Shugaba Donald Trump ya ce an cimma matsaya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batun makamin nukiliyarta wanda aka shafe shekaru ana tababa.

Kalaman Trump sun nuna yiwuwar Iran ta ci gaba da riƙe sinadarin uranium da ta tace a boyayyun wurare duk da bai fayyace ba.

Trump ya jaddada cewa Iran ta amince ba za ta mallaka, saya ko ƙera makamin nukiliya ta kowace hanya ba inda ya tabbatar da cimma matsaya kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.