'Ni ne Gatansa': Trump Ya Fusata kan Cewa Netanyahu Ya Jawo Shi cikin Yaki da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi karin haske game da jita-jitar cewa Benjamin Netanyahu ne ya visa shi a yaki da Iran
- Trump ya musanta zargin da ake yada wa game da yaki da Iran inda ya bayyana cewa shi ne ya fara daukar matakin
- Ya kuma tabbatar da cewa ya yi magana mai zafi da Netanyahu saboda rashin jin dadinsa kan ci gaba da rikicin Isra'ila da Lebanon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana damuwa kan jita-jitar da ake yadawa kansa game da yaki da Iran.
Trump ya yi ikirarin cewa da ba saboda shi ba, da Isra'ila ba za ta kasance kamar yadda take a yau ba.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Pod Force One da The Independent ta bibiya inda ya mayar da martani kan zargin cewa an jawo shi rikici da Iran.
Trump ya tsage gaskiya kan shiga yakin Iran
Da aka tambaye shi ko Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yaudare shi, Trump ya ce shi ne ya fara daukar matakin da kansa.
Ya ce matakin ya samo asali ne daga damuwarsa kan yunkurin Iran na mallakar makamin nukiliya wanda yake ganin babban barazana ne.
A cewarsa, ba za a iya barin Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma da ba saboda shi ba, Isra'ila ba za ta wanzu ba.
Kalaman nasa sun zo ne a lokacin da ake rahotannin rashin jituwa tsakaninsa da Netanyahu bayan wata tattaunawar waya da suka yi.
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar ta shafi hare-haren sojin Isra'ila da kuma ci gaba da rikice-rikicen yankin Gabas ta Tsakiya.
Trump ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya fusata yayin wata tattaunawa da Netanyahu game da rikicin Isra'ila da Lebanon.

Source: Getty Images
Cacar baki tsakanin Trump da Netanyahu
A wata hira da aka wallafa, an tambaye shi ko ya yi amfani da kalamai masu zafi wajen magana da Netanyahu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
"Asiri zai tonu," Ana zargin ba tsakani da Allah Kwankwaso ya hada kai da Peter Obi ba
Trump ya tabbatar da cewa hakan gaskiya ne, yana mai cewa ya gaji da yadda rikicin da Lebanon ke ci gaba ba tare da tsayawa ba.
Ya ce ya gaya wa Netanyahu cewa lokaci ya yi da ya kamata a dakatar da rikicin domin samar da zaman lafiya.
Trump ya kira Netanyahu da sunan lakabinsa na "Bibi", yana mai jaddada cewa dole ne a kawo karshen rikice-rikicen da ake fama da su.
Wannan furuci ya sake jawo hankalin jama'a kan dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu da kuma matsalolin tsaron yankin.
An ji hirar Trump da jami'ansa kan yakin Iran
A baya, an ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa wasu manyan mataimakansa a sirrance cewa ba zai cigaba da musayar wuta da Iran a fagen daga ba.
Duk da yawaitar arangama a yankin, jami’an sun ce yarjejeniyar dakatar da kai hare-haren sama da aka shafe makonni ana aiwatarwa tana nan daram.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ke cewa sun kusa cimma yarjejeniya da Iran domin kawo karshen yakin da suka fara a Fabrairun 2026 gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
