‘Ba a Ji Komai ba, Abin da Ke Ciki Ya fi Zafi’: Rarara kan Wakar ‘Pantami’
- Fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya yi martani game da wakarda ya fitar wacce ta jawo maganganu a tsakanin alumma
- Rarara ya bayyana cewa wakar siyasa ce ta yabon dan takararsa da gwamnan Gombe, yana jaddada cewa bai yi nufin cin mutunci ba
- Mawakin ya ce shi almajirin malamai ne kuma yana girmama su, amma ya soki malaman da ke amfani da zagi maimakon wa'azi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitaccen mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi martani bayan sukar wakar da ya fita kan siyasar Gombe.
Mawakin ya bayyana cewa shi bai kira sunan kowa ba da mutane za su ce malam ya ce, ya ce duk wanda ya tsargu shi ya so.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da aka yi hira da shi wanda shafin DCL Hausa ta wallafa a Facebook a yau Asabar 1 ga watan Agustan 2026.
'Mai zafin na zuwa' - Rarawa ya yi martani
A cikin bidiyon, Rarara ya ce abin da aka ji daga cikin wakar ba komai ba ne idan aka kwatanta da abin da ke cikinta.
Ya bayyana cewa babu sunan wani da ya kira a cikin wakarsa da za a ce da wani yake yi, amma duk wanda ya tsargu shi jawo wa kansa.
A cewarsa:
"Ni dai na yi waka, na ce 'malam ka yi rawa, ba wai ba', amma ni ban ce wane na yi wa waka ba, ko wane, kin san riga ce ba wuya, wanda ya ga zata masa daidai ya dauka ya saka, wannan gare shi.
"Amma ni na yi waka ta siyasa, na yabi dan takara ta, na yabi gwamnan Gombe a ciki amma ni bance da wane nake yi ba.
"Na ce malam ka yi rawa, watakila wani malamin ya yi, wannan ya rage nasa, ba a fa aki wakar ba, kidan wakar ce fa sake, ai abin da ke cikin wakar ya fi rigima, daga kisan waka har an fara maganganu.
"Wanda ya ce da malam? wannan kuma ya rage na su, ni dai bance wani malam ba, malam kawai na ce, malami ya kira wani da fasiki ko dan iska, wannan ba wa'azi yake yi ba saboda babu aya ko hadisi da ya yarda da haka, akwai irin wadannan malaman."

Source: Facebook
Rarara ya ce shi dan gidan malamai ne
Mawaki Rarara ya bayyana yadda ya taso a gidan malamai inda ya ce tabbas yana mutunta malamai a matsayin iyayensa yake kallonsu.
Sai dai ya cewasu malaman suna sauka daga kan hanya duba da yadda suke zagin wasu mutane ko yan uwansu malamai.
Ya ce:
"Nima almajirin malam ne, dan malam ne, kakana malami ne, haka ma babana, kin ga ni duk wanda ya ce shi malam ne, ba zai nuna mun malanta ba.
"Da yawa malaman da ke suka ma bana kula su saboda ina kallonsu a matsayin iyayena, amma idan na fuskanci ka sauka a layi, wannan ba wa'azi ba ne"
Rarara zai shiga yankin Arewa tallata Tinubu
A wani labarin, an ji cewa wasu mambobin tafiyar Triple R sun yi bankwana da kungiyar bayan rikicin da ya taso kan rabon kudi da aka karbo daga 'yan siyasa.
Rahoto ya nuna cewa sakataren kungiyar, Ahmed Bifa ya amince an karbi kudi amma ya musanta cewa kudin ne ya fi muhimmanci a tafiyar.
Bifa ya bayyana cewa tsohon gwamnan Zamfara ya ba tafiyar kudi har Naira miliyan 500 domin tallata shugaban kasa Bola Tinubu a 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng


