'Maganar Nukiliya Ta Kau': Trump Ya Sha Alwashi kan Ƙasar Musulunci Ta Iran
- Shugaba Donald Trump ya ce an cimma matsaya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan batun makamin nukiliyarta wanda aka shafe shekaru ana tababa
- Kalaman Trump sun nuna yiwuwar Iran ta ci gaba da riƙe sinadarin uranium da ta tace a boyayyun wurare duk da bai fayyace ba
- Trump ya jaddada cewa Iran ta amince ba za ta mallaka, saya ko ƙera makamin nukiliya ta kowace hanya ba inda ya tabbatar da cimma matsaya kan haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake yin magana game da makamin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Trump ya tabbatar da cewa sun samu matsaya game da shirin makamin nukiliyar kasar a yakin da ake yi.

Source: Getty Images
Trump ya magantu kan makamin nukiliyar Iran
Rahoton Al Jazeera ya tabbatar da cewa Trump ya ce Iran ba za ta samu damar mallakar makamin ba.
Trump ya ce babu wani maganar kera makamin nukiliya inda ya tabbatar da cewa sun cimma matsaya game da yakin da ya ki ci ya ki cinyewa.
An tambayi Shugaba Donald Trump kan cikakkun bayanai game da wannan takardar yarjejeniya yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.
Trump ya amsa da cewa:
"Eh, mun cimma matsaya a matakin tunani kan wannan batu, kuma babu wanda zai iya kusantar wurin saboda an binne shi a ƙarƙashin wani dutse."

Source: Getty Images
Abin da Iran za ta iya rikewa
Kalaman shugaban sun bar yiwuwar cewa Iran za ta iya ci gaba da riƙe uranium da ta tace wanda aka ɓoye a ƙarƙashin ƙasa, sai dai bai yi ƙarin bayani ko fayyace matsayin ba, cewar rahoton CBS News.
Wannan magana ta Trump ta nuna irin kwarin gwiwar da shugaban ke da shi game da matsayar da ya ce sun cimma a yakin da aka shafe fiye da watanni uku ana yi.
An sake matsa masa da tambaya kan ko Iran ta amince cewa ba za ta mallaki makamin nukiliya ba wanda yana daya daga cikin musabbabin fara wannan yaki ake yi tun a karshen watan Fabrairun 2026.
Sai Trump ya ce:
"Ba za su mallaki makamin nukiliya ba. Sun amince da hakan."
"Ba wai kawai ba za su mallaka ba ne, ba za su saya ko ƙera shi ta kowace hanya ba, ko ta kowace siga. Ba za su mallaki makamin nukiliya ba."
An bukaci a Amurka ta mika wuya
A wani labarin, an ji cewa wani dan majalisar Iran, Ebrahim Rezaei ya ce al'ummar Iran ba za su amince da mika wuya ba, yana mai cewa Amurka ce ya kamata ta mika wuya.
Kakakin kwamitin tsaro na majalisar Iran ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump yana da zabuka biyu kacal, kuma dukansu mika wuya ne.
Rundunar sojin Iran ta ce za ta ci gaba da mayar da martani kan harin Amurka, tare da rufe mashigan Hormuz wanda ke da tasiri matuka kan tattalin arzikin duniya.
Asali: Legit.ng

