Amarya Ta Zo da Sabon Salo, Ta Je wajen Bikin Aurenta a kan Saniya
- Wata amarya mai suna Victoria Lee ta isa wurin bikin aurenta a ƙauyen Mark da ke kusa da Burnham-On-Sea a kan ɗaya daga cikin shanunta
- Victoria, mai shekaru 37, ta ce tana son saniyarta mai suna White Chocolate Button ta kasance cikin babban ranarta saboda “ita ce kusan babbar ƙawa ta”
- Bayan an kammala bikin, Victoria da mijinta Mike sun koma gona domin yin aikin tatsar shanu kafin daga bisani su koma wajen bikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Ingila - Baƙi da suka halarci wani bikin aure a ƙauyen Mark da ke kusa da Burnham-On-Sea sun ga wani abin da da wuya za su manta da shi, bayan amarya Victoria Lee ta isa wajen bikin aurenta a kan ɗaya daga cikin shanunta.
Manomiyar mai shekaru 37 ta ce tana son saniyar mai suna White Chocolate Button ta kasance cikin babban ranarta saboda “ita ce kusan babbar ƙawa ta”.

Source: Twitter
Victoria, wadda ta taso a gonar iyalinta da ke Dorset, ta ce tun tana yarinya take hawa shanu bayan an gaya mata cewa ba za ta iya samun doki ba, cewar rahoton shafin burnham-on-sea.com
Amarya ta zabi zuwa wajen aurenta a ka saniya
Lokacin da take shirin bikin aurenta, ta yanke shawarar cewa White Chocolate Button ce za ta ɗauke ta zuwa coci.
Ta ce ta kuma yi ƙoƙarin horar da wata saniya mai suna Basil, amma “ba ta son yin hakan… ta yi ƙoƙarin jefo ni daga bayanta”, don haka ta yi watsi da wannan ra’ayin cikin gaggawa.
Saniyar ta saba da ado
White Chocolate Button ba baƙuwa ba ce wajen jan hankali a gonar, domin a baya ma an taɓa saka ta cikin bukukuwan Halloween.
Victoria ta ce:
“Ana sanya mata zanin gado a jikinta, sannan a yanke mata guraben ido da kunnuwa, don haka ta saba da sanya kaya.”
An ɗauki amaryar zuwa ƙauyen Mark a kan tarakta, kafin ta ƙarasa sauran tafiyar zuwa coci a kan saniyarta, yayin da ƙawayen amaryar suka kewaye ta suna tafiya tare da ita.
Bayan kammala bikin, samarin da suka yi wa ango hidima suka tsaya a wajen cocin suna girmama ma’auratan, inda suka ɗaga wasu kayan aikin gona sama.

Source: Twitter
Yayin da baƙi suka nufi wurin liyafa, Victoria da mijinta Mike suka koma gona domin tatsar shanu, inda suka bar abokai da ’yan uwa suna shagalin kansu na tsawon wasu sa’o’i.
Daga bisani ma’auratan suka koma wajen bikin suka ci gaba da murnar aurensu, amma White Chocolate Button ta kasance a gona domin samun hutun da ta cancanta.
Haruna Bashir ya yi sabon aure
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutumin da ya rasa matarsa da 'ya'yansa shida bayan an kashe su a farkon shekarar nan, Haruna Bashir, ya sake yin aure a karkashin shirin auren gata da gwamnatin jihar Kano ta shirya wa ma'aurata 1,500.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya wakilci ango a matsayin waliyyi, yayin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya wakilci amaren.
Asali: Legit.ng

