Jirgin Dakon Mai Ya Gamu da Iftila'i, An Buɗe Masa Ruwan Wuta a Mashigar Hormuz
- Wani jirgin dakon mai ya fuskanci mummunan hari a lokacin da ya fara wucewa ta mashigar Hormuz da ke ƙasar Iran
- Hukumar Birtaniya da ke kula da harkokin kasuwanci ta teku ta tabbatar da harin da aka yi amfani da wasu irin makamai da ba a sani ba
- Hukumar ta bayyana halin da ma'aikatan jirgin ke ciki da kuma muhalli ganin yadda akan kai harin kai jirgi mai dakon mai da zai iya gurbata muhalli
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran– Wani jirgin dakon mai ya gamu da hari a mashigar ruwa ta Hormuz bayan an harbe shi da wasu abubuwa da har yanzu ba a tantance samfurin makaman ba.
Wannan na zuwa ne a wani sabon yanayi na ƙara tashin hankali a yankin tekun da ke Gabas ta Tsakiya yayin da ake kwan-gaba-kwan-baya kan yakin Amurka da Iran.

Source: Facebook
Al-Jazeera ta ruwaito cewa hukumar Birtaniya da ke kula da harkokin kasuwanci ta teku (UKMTO) ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da gabar tekun Fujairah a ƙasar UAE.
An kai wa jirgin mai hari a Hormuz
Kafar Reuters ta wallafa cewa hukumar UKMTO ta bayyana cewa jirgin ya fuskanci abin da ta kira harbin wasu abubuwa da ba a san su ba, wato an yi amfani da bakin makamai a harin.
A cewar rahoton hukumar, duk da harin, babu wanda ya jikkata daga cikin ma’aikatan jirgin, kuma an tabbatar da cewa dukkaninsu na cikin koshin lafiya.
Haka kuma, babu wani rahoto da ke nuna cewa an samu wata matsala ta gurɓatar muhalli sakamakon harin da aka kai wa jirgin ruwan.
Mashigar Hormuz dai na daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai a duniya, inda manyan jiragen dakon mai ke ratsa kowace rana.
Duk wani tashin hankali a wannan wuri na iya yin tasiri kai tsaye ga kasuwannin makamashi na duniya saboda za a samu tsaikon zirga-zirgar mai.
Ba a san wa ya kai hari Hormuz ba
Wannan hari ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan hukumar UKMTO ta sanar da wani hari daban da aka kai wa wani jirgin dakon kaya a kusa da gabar tekun Iran.
Rahotanni sun nuna cewa wasu ƙananan jiragen ruwa da dama ne suka kai hari kan jirgin, wanda ke tafiya a kusan kimanin kilomita 18 daga yammacin garin Sirik.

Source: Getty Images
Ba a bayyana cikakken bayani kan yadda harin ya gudana ba, amma lamarin na ƙara jaddada damuwar da ake da ita kan tsaro a yankin, musamman ganin yadda hare-hare kan jiragen ruwa ke ƙaruwa a wannan lokaci.
Masana harkokin tsaro na teku sun dade suna gargadin cewa yankin mashigar Hormuz na fuskantar barazana sakamakon rikice-rikicen siyasa da ke gudana a yankin.
Duk wani hari irin wannan na iya janyo martani daga ƙasashe masu ruwa da tsaki, tare da yiwuwar ƙara tsananta rikicin Gabas ta Tsakiya.
Har yanzu dai babu wata ƙungiya ko ƙasa da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma tabbatar da tsaron jiragen ruwa da ke wucewa a yankin.
Trump zai tura sojoji Hormuz
A baya, mun wallafa cewa ana cigaba da takaddama tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya musamman yayin da aka gaza cimma matsaya kan mashigar Hormuz.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce kasar shi za ta taimaka wajen fitar da jiragen ruwa da suka makale daga mashigar da Iran ta toshe don hana jirage wuce wa.
Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta toshe mashigar Hormuz ne tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka hada kai suka kai mata a karshen watan Fabrairun 2026.
Asali: Legit.ng


