Tirkashi:An Ji Dalilin da Ya Sa Kakakin White Houae Ta Bar Gwmanatin Trump, 'Ba Zan Iya ba'
- Karoline Leavitt ta sanar da cewa za ta bar gwamnatin Shugaba Donald Trump a ƙarshen Agustan 2026
- Tun da farko Shugaba Donald Trump ya ce kakakin mai shekaru 28 za ta bar aikinta a fadar White House ta kasar Amurka
- Donald Trump ya ce Leavitt za ta ci gaba da kasancewa cikin manyan masu ba shi shawara a wajen gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Karoline Leavitt, sakatariyar yaɗa labarai ta Fadar White House, ta sanar da cewa za ta bar gwamnatin Donald Trump a ƙarshen Agusta domin ta samu ƙarin lokaci da za ta kula da ƙananan ’ya’yanta.
Leavitt, mai shekaru 28, ita ce mafi ƙaramar mutum da ta taɓa riƙe muƙamin sakatariyar yaɗa labarai ta Fadar White House.

Source: Twitter
Leavitt ta tabbatar da cewa za ta bar mukamin na ta ne a wani rubutu da ta yi a shafinta na X a ranar Laraba, 12 ga watan Agustan 2026.
Taa bayyana matakin a matsayin “shawarar da ke ɗauke da ɗaci” jim kaɗan bayan Shugaba Donald Trump ya tabbatar da cewa za ta bar muƙamin.
Sanarwar ta zo ne bayan watanni kaɗan da Leavitt ta koma ɗakin taron manema labarai na Fadar White House bayan ta haifi ɗanta na biyu, wata ’ya mace mai suna Viviana, a watan Mayu. Haka kuma tana da ɗa namiji mai shekaru biyu.
Dalilin Karoline na barin Fadar White House
Leavitt ta ce yawan buƙatun da aikinta ke da su ya sa yake da wahala ta daidaita shi da rayuwar iyalinta.
Ta rubuta cewa tun bayan da ta koma Fadar White House bayan haihuwar ’yarta, ta fahimci cewa ba za ta iya zama uwa mafi nagarta ga ƙananan ’ya’yanta biyu ba tare da ba da lokaci, ƙarfi da kulawar da muƙamin sakatariyar yaɗa labarai ke buƙata a kai a kai ba.
Ta ce hakan ne ya sa a ƙarshe ta yanke shawarar barin Fadar White House tare da fara wani sabon babi a rayuwarta.
Trump bai sanar da magajinta ba
Trump bai bayyana wanda zai maye gurbin Leavitt a wannan muƙami mai matuƙar tasiri ba.
A nasa saƙon da ya wallafa a kafar sada zumunta, shugaban ya ce yana mutunta shawarar Leavitt, sannan ya nuna cewa za ta ci gaba da kasancewa cikin masu ba shi shawara kan harkokin siyasa.
Trump ya ce Leavitt za ta kasance ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara a wajen gwamnati, tare da kasancewa murya mai tasiri a cikin Jam’iyyar Republican yayin da suke aiki domin samun gagarumar nasara a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki.
Tarihin Leavitt a siyasa
Vanguard ta ce kafin ta zama sakatariyar yaɗa labarai, Leavitt ta yi aiki a matsayin mai magana da yawun MAGA Inc., wata ƙungiyar siyasa mai zaman kanta da ke goyon bayan Trump. Daga bisani ta shiga yaƙin neman zaɓen Trump na shekarar 2024.
A shekarar 2022, Leavitt ta nemi a zaɓe ta zuwa wani muƙami na siyasa, inda ta yi nasara a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar Republican a tsakanin ’yan takara 10 domin neman kujerar Majalisar Wakilan Amurka daga New Hampshire.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta kafa tarihi, ta kawo sababbin dokoki game da talla a Najeriya
Sai dai daga baya ta sha kaye a babban zaɓen daga hannun Chris Pappas, ɗan takarar Jam’iyyar Democrat mai riƙe da kujerar.
Leavitt ta taɓa aiki a ofishin yaɗa labarai na Fadar White House a wa’adin farko na Trump, kafin daga bisani ta zama daraktar yaɗa labarai ta Elise Stefanik, ’yar Majalisar Wakilan Amurka daga Jam’iyyar Republican mai wakiltar New York.

Source: Twitter
Trump ya yi basaja
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da cewa ya yi basaja saboda tsoron barazanar Iran.
Shugaba Donald Trump ya tabbatar da cewa ya sauya jirgi a asirce bayan ya bar taron kungiyar NATO a kasar Turkiyya.
Asali: Legit.ng

