Yaki Ya Barke: Iran da Isra'ila na Yi wa Juna Barin Wuta da Safiyar Yau

Yaki Ya Barke: Iran da Isra'ila na Yi wa Juna Barin Wuta da Safiyar Yau

  • Isra'ila ta kaddamar da hare-haren sama da sanyin safiyar Litinin kan Iran a matsayin martani ga harbo makamai masu linzami daga Tehran
  • Tashar talabijin ta Gwamnatin Iran ta ruwaito cewa an ji karar fashewa a Isfahan, Karaj, Tabriz da Tehran, ba tare da yin ƙarin bayani ba
  • Iran ta kara kai hare-hare Isra'ila ranar Litinin, lamarin da ke barazanar sake jefa Gabas ta Tsakiya cikin wani sabon yaƙi a yankin baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Isra'ila - Kasar Isra'ila ta kai hare-haren sama a Yammaci da wasu yankunan Iran, bayan Tehran ta harba makamai masu linzami zuwa Arewacin Isra'ila.

Wannan ne karo na farko da Iran da Isra'ila suka kai hare-hare cikin yankunan juna tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta watanni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bayan an ja kunnen Netanyahu, Iran ta kai harin makamai masu linzami zuwa Isra'ila

Harin da Iran ta kai zuwa Isra'ila
Makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton The Guardian ya bayyana cewa Iran ta kaddamar da hare-haren ne bayan Isra'ila ta kai farmaki ta sama a Beirut da ke Lebanon a ranar Lahadi.

Isra'ila ta kai hari a kasar Iran

Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta kai hare-hare kan wurare da dama a wata cibiyar sarrafa sinadarai daga man fetur ta Iran da ke Mahshahr, a Kudu maso yammacin ƙasar.

Rundunar IDF da kafafen yaɗa labaran Gwamnatin Iran sun tabbatar da harin, inda kafafen Iran suka ce cibiyar da ke kusa da Arewacin gabar Tekun Farisa ta samu wata 'yar matsala.

Iran ta harba makamai Isra'ila

BBC ta wallafa cewa Iran ta sake harba makamai zuwa Isra'ila a safiyar yau bayan rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan wuraren soji a Tsakiya da Yammacin Iran da sanyin safiyar yau.

Sabuwar musayar hare-haren ta zo ne duk da rahotannin cewa shugaba Donald Trump ya gaya wa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da ya guji kai hari kan Iran.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai harin da ya yi barna mai girma a tsakiyar Israila

Isra'ila ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga harin makami mai linzami da Iran ta kai Arewacin Isra'ila jiya — wanda shi ma ya kasance martani ga hare-haren Isra'ila kan Hezbollah a Beirut.

Wuraren da aka kai hari Lebanon
Hayaki na tashi a wuraren da Isra'ila ta kai hari Lebanon. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan shi ne karo na farko da Isra'ila ta kai hari kan Iran tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta daidai watanni biyu da suka gabata.

Bayanan da aka samu sun ce kafafen yaɗa labaran Gwamnatin Iran sun ruwaito fashe-fashe a garuruwan Tehran, Isfahan, Tabriz da Najafabad.

Iran ta auka wa Isra'ila saboda taba Lebanon

A wani labarin, mun kawo muku cewa a daren jiya, Iran ta harba jerin makamai masu linzami zuwa Arewacin Isra'ila, karon farko tun bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilun 2026.

Iran ta zargi Isra'ila da karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hari kan Hezbollah a Kudancin yankunan Beirut — inda aka ruwaito cewa aƙalla mutum biyu sun mutu.

Rundunar sojin Isra'ila ta yi ikirarin cewa ta kai hare-haren ne a matsayin martani ga harba rokoki da Hezbollah mai samun goyon bayan Iran ta yi zuwa Arewacin Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng