Iran: 'Ana Kokarin Goga Mana Kashin Kaji kan Harin Saudiyya'

Iran: 'Ana Kokarin Goga Mana Kashin Kaji kan Harin Saudiyya'

  • Daular Musulunci ta Iran ta yi martani game da harin da aka ce ta kai wasu muhimman wurare a kasar Saudiyya ana tsaka da batun tsagaita wuta
  • Wani jami'in soji ya ce jingina duk wani hari kan kadarorin kasar Amurka ga Iran kuskure ne babba, musamman a wannan lokaci mai sammatsi
  • Kalaman sun biyo bayan zargin da Saudiyya ta yi wa ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a Iraki yayin da yaki ke kara kacamewa a yankin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Iran – Wani babban jami'in soja na Iran ya bayyana cewa su na Allah wadai da zargin cewa Tehran na da alaƙa da makaman da aka harba daga wata ƙasa zuwa wasu wurare a Saudiyya.

Kara karanta wannan

An kama matashi da buhunan abinci da wasu muhimman kaya zai kai wa Boko Haram

Ya musanta hakan ne jim kadan bayan wasu manyan hare-hare a kan kadarorin Amurka da ke kasa mai tsarki, kuma aka jingina masu ita.

Iran ta nesanta kanta da kai hari Saudiyya
Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran, Yariman Saudiyya Muhammad Bn Salman Hoto: Inside the Haramain, Anadolu Ajansi
Source: Getty Images

Aljazeera ta kawo labarin cewa Saudiyya ta bayyana cewa Iran na da alaka da hare-haren da aka kai kasarta duk da ana maganar tsagaita wuta.

Iran ta kare kanta daga zargin Saudiyya

Jami'in ya ce, Iran ta yi watsi da duk wata alaƙa da makaman da aka harba daga wasu ƙasashe zuwa wuraren da aka kai wa hari a Saudiyya.

Ya kuma ƙara da cewa:

"Jingina duk wani hari kan muradun Amurka a yankin ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran babban kuskure ne, kuma hakan na nuna rashin fahimtar halin da yankin ke ciki."

Wannan martani ya zo ne bayan Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta sanar da cewa an sake kai hare-hare da jiragen marasa matuƙi kan cibiyoyin man fetur da ke Lardin Gabashin ƙasar.

Zargin da Saudiyya ke yi wa Iran

Ma'aikatar ta ɗora alhakin hare-haren kan ƙungiyoyin mayaƙa da ke Iraki waɗanda ta ce suna da alaƙa da Iran duk dai Iran ta musanta hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi wa sojoji albishir, Tinubu zai sanar da karin albashinsu

Iran ta ce kuskure ne a jingina mata harin Saudiyya
Shugaban kasar Saudiyya, Masoud Pazeshkian Hoto; Getty
Source: Getty Images

Ta ce an kai hari kan cibiyoyin man fetur da ke Lardin Gabas da yankin Riyadh. Amma an harbo jiragen ne daga ƙasar Iraki, kuma ƙungiyoyin ta'addanci masu alaƙa da Iran ne suka kai harin.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Masarautar Saudiyya ba ta neman rikici ko ƙara ta'azzara tashin hankali, amma za ta mayar da martani ga duk wani hari da aka kai mata."

Amurka da Saudiyya sun kai hari

A wani labarin, kun ji cewa kasashen Amurka da Saudiyya sun kai hare-hare kan kungiyoyin da Iran ke marawa baya a Iraki bayan hare-haren jiragen sama marasa matuki da ta ce an yi amfani da su.

Saudiyya ta ce jiragen kariyarta sun kakkabo jirage marasa matuki, tana zargin mayakan da Iran ke goyon baya da kai hare-haren daga cikin Iraki a kan wasu kadarori da ke da alaka da man fetur.

Kasashen biyu sun ce ba sa neman rikici, amma sun jaddada cewa za su kare kasashensu da kadarorinsu idan aka sake kai musu hari a Gabas ta Tsakiya da ke neman birkicewa a yanzu haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng