Shugabannin Igbo Sun Fadi Matsayarsu kan Alkawarin da Obi Ya Yi ga Kwankwaso
- Wasu jiga-jigan Igbo sun goyi bayan alkawarin Peter Obi na yin wa’adi ɗaya idan ya lashe zaɓen 2027 da ake tunkara a yanzu
- Shugabannin Ohanaeze sun ce Obi ba ya buƙatar neman amincewar Igbo kafin yanke shawarar siyasa, domin yana takara ne a matsayin ɗan Najeriya
- Ra’ayoyi sun bambanta kan yarjejeniyar Obi da Kwankwaso, inda wasu ke goyon baya, wasu kuma ke cewa wa’adi ɗaya ba zai amfani Kudu maso Gabas ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wasu fitattun shugabannin Igbo sun bayyana goyon bayansu ga alkawarin Peter Obi na yin wa’adi ɗaya kacal.
Peter Obi ya yi alkawarin ne idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, suna mai cewa matakin yana da amfani ga ƙasa baki ɗaya.

Source: Twitter
Shugabannin Igbo sun wanke Peter Obi

Kara karanta wannan
"Shiri ne": Yadda aka kashe babban soja mahaddacin Kur'ani mai shirin kafa tarihi
Tsoffin shugabannin ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Ichie Damian Okeke-Ogene da Cif Emeka Attamah, sun ce Obi yana neman shugabancin Najeriya ne a matsayin ɗan ƙasa, ba a matsayin ɗan takarar Igbo ba, cewar Leadership.
Sun bayyana cewa saboda haka ba lallai ba ne Obi ya nemi shawara ko amincewar shugabannin Igbo kafin yanke hukunci kan yadda zai gudanar da mulki idan ya yi nasara.
Attamah ya ce mai yiwuwa Peter Obi ya tattauna da shugabannin Igbo masu goyon bayan takararsa, yana mai cewa alkawarinsa ya dace da burin daɗe ana yi na ganin ɗan Igbo ya zama shugaban Najeriya.

Source: Facebook
Muhimmancin zaben kwararren shugaba a Najeriya
Okeke-Ogene ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙwarewar shugaba, ba tsawon lokacin mulki ba, cewar Tribune.
Ya tunatar da cewa marigayi Obafemi Awolowo ma ya taɓa cewa sa'o'i 24 sun isa ya fara gyara Najeriya.
Har ila yau, ya kuma ce alkawarin wa’adi ɗaya yana nuna girmama tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, wanda ya kasance al'adar siyasar Najeriya tsawon lokaci.
Sai dai kakakin Ohanaeze Ndigbo, Dakta Chukwu Ezechi, ya bayyana cewa shawarar yin wa’adi ɗaya ta Peter Obi da jam’iyyarsa ce kaɗai, ba matsayar Ohanaeze ba.
A Enugu da Abia kuwa, ra’ayoyi sun bambanta, wasu dattawan Igbo sun ce shekaru huɗu sun isa a kafa tubalin ci gaba, yayin da wasu suka soki yarjejeniyar saboda ba a yi cikakkiyar shawara da yankin Kudu maso Gabas ba.
Obi ya magantu kan rashin tsaro
Mun ba ku labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce da shi ne shugaban kasa da kansa zai shiga dajin da aka boye dalibai da malamai da aka sace a Oyo.
Obi ya ce ba zai jira sama da kwanaki 50 ba kafin daukar mataki, yana mai jaddada cewa jagoranci mai nagarta ne mabuɗin magance matsalar tsaro.
Ya kuma soki Shugaba Bola Tinubu kan rashin kiran gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a tsawon lokacin da aka shafe ana tsare da wadanda aka sace.
Asali: Legit.ng
