Yakin Iran: Amurka Ta Jefa Makamai, An Hallaka Jami'an Kasar Indiya

Yakin Iran: Amurka Ta Jefa Makamai, An Hallaka Jami'an Kasar Indiya

  • Yayin da aka ci gaba da ruwan ruwa a tsakanin Amurka, Isra'ila da kuma Iran, an hallaka wasu ma'aikatan ruwa a gabar ruwan Oman
  • Bayan hallaka jami'an,har yanzu ana neman mutum guda, wanda babban injiniya ne da ke aiki da gwamnatin kasar ta Indiya
  • Tuni gwamnati ta fara daukan mataki, inda ta gayyaci mataimakin jakadan Amurka a Indiya tare da nuna matukar rashin jin dadinta kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar India – Ma’aikatan ruwa ‘yan kasar Indiya uku sun rasa rayukansu yayin da wani mutum guda ya bace bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai.

Dakaraun Amurka sun kai kan jirgin dakon mai mai suna Settebello a gabar tekun Oman a daren ranar Talata 9 ga watan Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta harbo jirgin yakin Amurka, Trump ya sha alwashin ɗaukar fansa

Amurka ta hallaka jami'an kasar Indiya
Wasu daga cikin jiragen yakin Amurka a kan ruwa Hoto: @CENTCOM
Source: Twitter

Kafar Aljazeera ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka mutu sun hada da Aditya Sharma, wanda ke aiki a matsayin matashin jami’in sashen bene na jirgin, da kuma Shivanand Chaurasiya, ma’aikacin sashen injina.

Harin Amurka: Ana neman gawar jami'in kasar Indiya

Kafar Reuters ta ruwaito cewa har ila yau, babban injiniyan jirgin, Patnala Suresh, na daga cikin wadanda har yanzu ba a san inda suke ba bayan harin.

Bayan aukuwar lamarin, gwamnatin Indiya ta dauki mataki cikin gaggawa ta hanyar gayyatar mataimakin shugaban ofishin jakadancin Amurka a kasar, Jason Meeks.

Mahukuntan Indiya sun bayyana wa jami’in Amurkan matukar damuwarsu tare da gabatar da korafi mai karfi kan harin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan kasarsu.

Lamarin ya kara janyo ce-ce-ku-ce tsakanin kasashen biyu, musamman ganin cewa mutanen da abin ya shafa ma’aikatan ruwa ne da ke gudanar da aikinsu a lokacin da harin ya faru.

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, an gano tana sheke aya a otal bayan an tara N20m kudin fansa

Amurka ta kare matakin kai hari

Rundunar Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an gudanar da shi ne cikin tsari na musamman yayin da jirgin ke wucewa ta yankin Tekun Oman.

Amurka ta ce jami'an Indiya sun ki bin umarnin da aka ba su
Shugaban kasar Amurka a wani taro Hoto: @ayomairoese
Source: Twitter

A cewar rundunar, an yi zargin cewa jirgin na dauke da man kasar Iran, lamarin da ya sanya aka dauki matakin kai hari a kansa.

Sojojin Amurkan sun kuma yi ikirarin cewa ma’aikatan jirgin sun gaza bin umarnin da aka ba su daga dakarun Amurka kafin a kai harin.

Sai dai har yanzu ba a bayyana karin bayanai kan yadda harin ya faru ko kuma halin da sauran ma’aikatan jirgin suke ciki ba.

Mutuwar ma’aikatan ruwan ya kara tayar da hankula a tsakanin iyalansu da kuma kungiyoyin ma’aikatan ruwa a Indiya, yayin da ake ci gaba da neman cikakken bayani kan abin da ya janyo harin da kuma sakamakonsa.

Amurka ta jawo an rufe Hormuz

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta sanar da rufe mashigar Hormuz gaba ɗaya ga dukkannin jiragen ruwa da ke son wucewa ta hanyar bayan sabon rikcin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Biyo bayan lamarin, rundunar sojin ruwan Iran ta kai hari kan wasu jiragen kasuwanci biyu da suka yi ƙoƙarin wucewa ta hanyar da ta ce ta rufe kirif Rahotanni sun nuna cewa an ji ƙarar fashewar makamai a biranen gabar teku na Bandar Abbas da Sirik da kuma tsibirin Qeshm da ke kusa da mashigar Hormuz Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng