Alaka Ta Yi Tsami: Trump Ya Zazzagi Netantahu kan kai Hare Hare Lebanon

Alaka Ta Yi Tsami: Trump Ya Zazzagi Netantahu kan kai Hare Hare Lebanon

  • An ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya fusata da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu yayin wata tattaunawar waya
  • Trump ya yi wa Netanyahu maganganu marasa dadi tare da matsa masa lamba ya amince da tsagaita wuta da kungiyar Hezbollah ta Lebanon
  • Haka kuma, shugaba Trump ya yi ikirarin cewa yana bin Netanyahu bashi saboda shi ne ya taimaka wajen hana a daure shi a duniya a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zama sanadin yadda duniya ke kara tsanar Isra’ila a wata tattaunawar waya mai zafi da suka yi a ranar Litinin.

Tun da farko a ranar Litinin, Iran ta yi barazanar dakatar da tattaunawarta da Amurka saboda matakan da Isra’ila ke dauka a Lebanon, lamarin da ya haifar da kiran wayar.

Kara karanta wannan

Trump ya hana Netanyahu kai hari Lebanon bayan waya da Hezbollah

Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu
Donald Trump a hagu da Benjamin Netanyahu a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar rahoton Jerussalem Post, a yayin tattaunawar, Donald Trump ya yi wa Netanyahu tsawa yana cewa 'me kake yi ne?”

Trump ya zazzagi Netanyahu

A cewar wani jami’in Amurka, Trump ya ji cewa Netanyahu yana mayar da martani fiye da kima kan hare-haren da Hezbollah ke kai wa Isra’ila.

Ya nuna adawa da yadda Isra’ila ke rusa gine-gine domin kashe kwamandan Hezbollah guda daya, da kuma barazanar da take yi wa birnin Beirut, in ji Axios.

Wata majiya ta kuma takaita wani bangare na kalaman Trump da cewa:

“Yanzu kowa ya tsane ka. Kowa ya tsani Isra’ila saboda kai.”

Trump ya kuma zargi Netanyahu da rashin nuna godiya, inda majiyar ta ce Trump ya yi ikirarin cewa da ba shi ba, da tuni an daure firaministan.

An soke hare-hare zuwa Beirut

Duk da cewa Netanyahu ya fitar da sanarwa bayan tattaunawar yana cewa matsayin Isra’ila “bai canza ba,” wani jami’in Amurka ya shaida cewa Trump ya yi nasara sosai a kan Netanyahu a tattaunawar.

Kara karanta wannan

An kai Trump asibiti domin duba lafiyar shi, likita ya fadi sakamakon bincike

Jami'in ya ce:

“Bibi ya ce, ‘To shikenan, to shikenan, kawai ka tabbatar an kula da komai,”

Wani jami’in ya ce wannan na daga cikin mafi munin tattaunawar da Trump ya taba yi da Netanyahu tun bayan fara wa’adinsa na biyu.

Bayan kiran wayar, Trump ya sanar da cewa Netanyahu ya janye sojojinsa, bayan ya bukace shi da kada ya kai wani babban hari kan Beirut.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump na bayani a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

A wani sako na dabam da ya fitar, Donald Trump ya rubuta cewa tattaunawa da Iran na ci gaba cikin gaggawa sosai.

Ana so Isra'ila ta bokarewa Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa ministan tsaron cikin gida na Isra’ila, Itamar Ben Gvir, ya bukaci Netanyahu da ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon.

Bayan Trump ya yi umarnin dakatar da kai hari Lebanon, Ben Gvir ya zuga Netanyahu da cewa yanzu ne lokacin da za a gaya wa shugaban Amurka a’a.

Ya ce yanzu ne lokacin yin abin da ya zama wajibi kuma dole, wato kai wa Hezbollah hari, bai wa mayaƙan Isra'ila cikakken ikon kai hare-hare Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng