Trump Ya Tabbatar da Ya Sauya Jirgin Sama a Asirce a Tafiyarsa saboda Tsoron Iran
- Jami’an tsaron Amurka sun gano barazana daga Iran, wanda ya sa aka fice da shugaban ƙasa a asirce daga jirgin sama
- Donald Trump ya sulale daga Air Force One zuwa ƙaramin jirgin soja na C-32A ta hanyar amfani da wata motar abinci
- Shugaba Trump ya tabbatar da hakan, ya ce kasancewar akwai barazanar tsaro daga ƙasar Iran ya canza jirgi a Turkiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya tabbatar da cewa ya sauya jirgin sama a yayin tafiya saboda barazanar Iran.
Donald Trump ya sauka daga jirgin samansa, ya shiga wani dabam yayin da yake dawo wa daga wata tafiya daga Turkiyya a watan Yuli.

Source: Getty Images
Donald Trump ya tabbatar da abin da ya faru
Shugaban Amurkan ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa ya sauya jirgi daf da za a tashi saboda mataki na tsaro a cewar tashar DW.
Mista Donald Trump ya fadi da bakinsa cewa an dauki matakin ne saboda gudun kasar Iran ta kawo wa shugaban Amurka hari.
An ji shi a bidiyo yana mai cewa ya bi umarnin jami’an tsaron farin kaya da sojoji ne, hakan ba ra’ayin kashin kan shi ba ne.
“Ina aiki da jami’an tsaron farin kaya da sojoji ne. Sun so in canza tafiya, a bi wani jirgin saman. Ina yin abin da suka ce ne kawai.
“Ina tunanin akwai barazana ne. Ban yi wasu dogayen tambayoyi a kai ba. Duk wani shugaban kasa mai tasiri yana fuskantar barazana sosai.
Duk da karfin wannan barazana, shugaban Amurkan ya nuna bai tsoron wani abu daga magauta yayin da yake sararin samaniya.
Rahotanni sun ce an yi hakan ne da nufin guje wa yunkurin kashe Mai girma Donald Trump, barazanar ta fito ne daga kasar Iran.
“Maganar gaskiya, ban damuawa da komai. Ko mene ne, kun san hali na, ko mene ne.”

Kara karanta wannan
Da gaske ne: Trump ya tabbatar da fargabar harin Iran, ya yi basaja a cikin jirgi
- Donald Trump
Yadda Donald Trump ya canza jirgi a hanya
A gida Premium Times ta samu labari Trump ya fice daga jirginsa na Air Force a boye, ya shiga wani jirgin sojoji da aka tanada.
Ya bar tsohon jirgin fadar shugaban kasa da ake kira presidential Jimbo jet, ya koma wannan jirgi na soji a wani yanayi na basaja.
Jaridar Washington Post ta bi kwa-kwaf, ta ce wannan jirgin sama shi ne na Air Force C-32A.

Source: Getty Images
Yadda Trump ya yi basaja a jirgi
Da aka fitar da sanarwa a ranar 8 ga watan Yuli 2026 lokacin da Trump zai koma gida, an sanar da tsarin tafiya a jirgin.
Bidiyoyi sun dauko Trump yana tafiya a babban birnin Turkiyya zai shiga jirgin samansa da ya kama hanyar Washington.
BBC ta ce jami’an gwamnati da ‘yan jarida sun dauka suna tare da Trump a dayan jirgin, ba su san ya rabu da su ba.
Da aka je shan mai a Ingila, sai aka ga Trump ya fito daga jirgin C-32A ya koma Air Force one da ya saba yin tafiya a ciki.
Canjin jirgin saman shugaban Amurka
Rahoto ya zo cewa harin Iran ya tsorata Donald Trump ya bar jirgin saman shi, wasu sun yi tunanin labarin bai tabbata.
Hakan yana zuwa ne bayan Amurka ta yi kwanaki 13 a jere tana kai hari kan kasar Iran a rikicin da aka dade ana yi.
Mai girma Trump ya bar Washington zuwa Ankara ne a Boeing 747-8 jumbo jet, wani jirgi da Qasar ta ba shi kyauta.
Asali: Legit.ng

