'Ba Mu Muka Kar Zomon ba': Hausawa Sun Yi Zanga Zanga bayan Sace Daliban Oyo
- Hausawa mazauna Ibadan da ke jihar Oyo sun gudanar da zanga-zangar lumana kan abin da suka kira nuna wariya da nuna masu kyama
- Lamarin ya kara kamari ne bayan wasu 'yan bindiga sun shuga makarantu uku a jihar tare da awon gaba da dalibai da malamansu da dama
- Wadannan Hausawan sun bayyana cewa ba su ga dalilin da ya sa za a rika dora masu laifin da ba su san hawa ko sauka ba a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Al’ummar Hausawa da ke zaune a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun fito zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadin nuna masu wariya.
Sun bayyana cewa nuna masu wariya da kyama a kan zargin da ake yi masu mara tushe bayan yawaitar sace-sacen mutane a jihar.

Kara karanta wannan
Dalibai sun tsere, iyaye sun kidime bayan jita jitar yan bindiga sun kutsa makarantu a Neja

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun taru da yawa a ranar Laraba, 9 ga watan Yuni, 2026 inda suka bayyana damuwarsu kan yadda wasu ke ɗora wa ɗaukacin Hausawa alhakin ayyukan masu aikata laifuffuka.
Hausawan da ke Oyo sun yi zanga-zanga
Sahara Reporters ta wallafa cewa Shugabannin al’ummar Hausawa sun ce bai kamata a yi amfani da laifuffukan wasu tsirarun bata-gari wajen yi wa kowa hukunci ko kallon dukkannin Hausawa a matsayin masu laifi ba.
Sun jaddada cewa mafi yawan Hausawan da ke rayuwa a Oyo mutane ne masu bin doka da oda, kuma su ma suna fama da matsalar rashin tsaro kamar sauran jama’ar jihar.
A cewarsu, abin da suke nema shi ne zaman lafiya da adalci ga kowa ba tare da la’akari da ƙabila ko yankin da mutum ya fito ba.
Dalilin zanga-zangar Hausawa a Oyo
Zanga-zangar ta biyo bayan fushin da ya daɗe yana ƙaruwa a tsakanin wasu mazauna jihar Oyo kan matsalar tsaro, lamarin da Hausawan suka ce ya haifar da tsangwama.

Source: Original
Sun yi zargin cewa ana jin haushin Hausawa, musamman ‘yan kasuwa da mazauna yankin da suka fito daga Arewacin Najeriya.
Tashin hankalin ya ƙara ƙamari ne bayan wani mummunan hari da ya faru a ranar 15 ga watan Mayun 2026 a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo.
A ranar, wasu ‘yan bindiga da suka sanya kayan sojoji sun kai hare-hare lokaci guda a makarantu uku da ke yankunan Yawota da Ahoro-Esinele da wasu al’ummomi da ke kusa.
Sheikh Gumi ya ziyarci jihar Oyo
A baya, mun wallafa cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana game da neman tsoma shi cikin lamarin sace dalibai da aka yi a wata makaranta a jihar Oyo,inda ya ce hakan sam bai dace ba.
Gumi ya bayyana cewa bai je Ibadan bisa gayyatar Musulman Kudu maso Yamma ba, illa wakiltar malaman Musulunci na Arewa bayan afkuwar mummunan lamarin da ya daga hankulan jama'a.
Malamin ya danganta sukar da aka yi masa da siyasar tsoron Musulunci, yana goyon bayan MURIC kan batun shari'ar Oyo tare da bayyana cewa babu wanda ya isa ya hana shi shiga jihohin kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
