Zanga Zanga: 'Yan Fansho Sun Yi Dana Sanin Saya wa Gwamna Kudin Sayen Fam

Zanga Zanga: 'Yan Fansho Sun Yi Dana Sanin Saya wa Gwamna Kudin Sayen Fam

  • Tsofaffin ma’aikata a a jihar Binuwai sun fusata, harsuka gudanar da zanga-zanga duk da ruwan sama saboda rashin biyan hakkokinsu
  • Sun ce har yanzu akwai bashin fansho da garatuti tun daga shekarar 2000 da gwamnatin jihar ta ki biyansu, ga shi sun yi mata hidima mai yawa
  • A martaninta, gwamnatin jihar ta ce ta gaji bashin fansho da garatuti da ya haura Naira biliyan 300 daga tsofaffin gwamnonin da suka shude

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue – Kungiyar 'yan fansho reshen jihar Binuwai ta gudanar da zanga-zanga a ranar Laraba 10 ga watan Yuni, 202 duk da ruwan sama mai karfi da aka samu.

Saun bayyana rashin jin dadinta kan rashin biyan garatuti da sauran hakkokin tsofaffin ma’aikata da suka ce sun dade suna jiran biya tun daga shekarar 2000.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai,an hallaka jami'an kasar Indiya

Yan fansho sun zargi gwamnan Binuwai da watsi da su
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia Hoto: Rev Fr Hyacinth Iormem Alia
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa kungiyar, wacce ta balle daga kungiyar NUP kuma aka yi mata rajista a shekarar 2022, ta fito kan titin Naka Road tare da 'ya'yanta dauke da alluna masu dauke da sakonni daban-daban na neman a biya su hakkokinsu.

Dalilin zanga-zanga a Binuwai

Jaridar Tribune Online ta wallafa cewa da yake zantawa da manema labarai yayin zanga-zangar, shugaban kungiyar, Akosu Orban, ya ce matakin ya biyo bayan gazawar Gwamna Hyacinth Alia wajen cika alkawurran da ya yi musu tun a shekarar 2022.

Orban ya bayyana cewa kungiyar ta taba hada kai da kungiyar masu baburan haya wajen tara kudin sayen fam din tsayawa takarar gwamna da na nuna sha’awa ga Alia kafin zaben 2023.

Ya bayyana cewa sun yi wannan kokari saboda fatan da suke da shi na cewa zai warware matsalolinsu idan ya hau mulki.

Sai dai ya ce yanzu suna nadamar wannan mataki saboda gwamnati ba ta cika alkawurran da aka yi musu ba kuma ta yi masu banza.

Kara karanta wannan

ESN ta shirya kai hare hare a wasu sassan Najeriya, DSS, sojoji sun dauki mataki

Yan fansho sun gargadi gwamnatin Binuwai

Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a biya bukatunsu ba cikin gaggawa, mambobin kungiyar za su iya mamaye gidan gwamnatin jihar domin nuna bacin ransu.

Shugaban kungiyar ya ce daga cikin matsalolin da suke fuskanta akwai bashin kudin fansho na watanni 38 ga wasu masu ritaya na gwamnatin jihar da kuma watanni 62 ga wasu na kananan hukumomi.

Yan fansho suna shirin mamaye gidan gwamnatin Binuwai
Taswirar jihar Binuwai, inda 'yan fansho ke zanga zanga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Orban ya kuma yi zargin cewa ba a daidaita kudain fansho yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanada ba.

A cewarsa, akwai masu ritaya da har yanzu suke karbar Naira 2,000 kacal a wata maimakon mafi karancin Naira 40,000 da aka amince da ita.

Ya kara da cewa wasu daga cikin masu ritayar sun shiga matsanancin hali sakamakon rashin biyan fansho da garatuti, lamarin da ya jefa iyalansu cikin wahala.

Gwamna ya sallami yan fansho

A wani labarin, kun ji cewa hukumar fansho ta Kano ta ce ta riga ta biya fiye da Naira biliyan 21 daga cikin bashin da tsofaffin ma’aikata ke bin gwamnatin jihar tun kafin wannan lokaci.

Kara karanta wannan

'Ba mu muka kar zomon ba': Hausawa sun yi zanga zanga bayan sace daliban Oyo

Shugaban hukumar, Alhaji Habu Fagge da ya bayyana haka, ya ce gwamnatinsu ta gaji bashin Naira biliyan 48.6 daga gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan koken tsofaffin ma'aikatan.

Hukumar ta zargi gwamnatin da ta gabata da cire kudin fansho ba bisa ka’ida ba, har ma da rance daga asusun fansho wanda hakan ya bar tsofaffin ma'aikatan da suka yi hidima a mugun hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng