Tinubu zai Wallafa Yadda aka Kashe Kudin da aka Samu daga Cire Tallafin Man Fetur
- Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta bayyana yadda ta yi amfani da kudaden da aka samu bayan cire tallafin man fetur
- Tinubu ya ce cire tallafin ya bai wa gwamnati damar karkatar da kudade zuwa wasu bangarorin tattalin arziki da ayyukan more rayuwa da ake gani
- Shugaban ya kuma bukaci NUPENG ta tabbatar da cewa lagwadar amfani da CNG ta isa ga fasinjoji, ba masu motocin dakon kaya kadai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ce gwamnatin tarayya za ta fitar da bayanai kan yadda ta yi amfani da kudaden da ta samu sakamakon cire tallafin man fetur.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis 13 ga watan Agusta, 2026 yayin da yake karbar shugabannin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NUPENG).

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Rahoton Amurka ya tabbatar da zargin Atiku kan gwamnatin Tinubu

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Tinubu ya kare matakin cire tallafin tare da bayyana irin ayyukan da gwamnati ta samar da kudaden gudanar da su.
Tinubu ya gana da NUPENG
Shugaban ya tuna da ganawar da ya yi da NUPENG kafin zaben shugaban kasa, inda kungiyar ta yi barazanar yajin aiki kan batun cire tallafin.
Ya ce tattaunawar da suka yi ta kasance tattaunawa mai matukar kyau, yana mai cewa tun kafin ya nemi takarar shugaban kasa ya bayyana matsayinsa kan batun tallafin.
Tinubu ya ce cire tallafin ya taimaka wa gwamnati wajen karkatar da kudade zuwa wasu bangarorin tattalin arziki, kuma nan ba da jimawa ba za a bayyana yadda aka yi amfani da su.
Tinubu ya kare tasirin cire tallafin
Shugaban ya kuma yi tir da masu cewa manufofin tattalin arzikin gwamnati ba su amfani talakawa, yana mai tambayar ko ma’aikatan kananan hukumomi da jihohi ba talakawa ba ne.
Ya ce biyan albashi a kan lokaci yana da tasiri ga tattalin arziki, domin kudaden da ma’aikata ke samu suna shiga kasuwanni tare da taimakawa iyalansu.

Source: Facebook
Ya ambaci hanyoyin Legas-Ibadan, Abuja-Kaduna, Abuja-Kano da Sokoto-Badagry, da kuma wasu manyan hanyoyin da ake ginawa a sassan kasar.
Tinubu ya ce:
“Duk wannan na amfaninmu ne, da amfanin tattalin arzikinmu da kuma tsaron mutanenmu."
Tinubu ya kuma bukaci NUPENG ta taimaka wajen ganin alfanun amfani da CNG sun isa ga fasinjoji. Ya ce a halin yanzu masu motocin dakon kaya ne suka fi amfana da rage kudin gudanarwa saboda amfani da gas din.
Kotu za ta zauna saboda Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sanya ranar 21 ga Satumba, 2026 domin sauraron karar da aka shigar da Shugaba Tinubu game da zaben 2027.
Kungiyar CFRPA ta nemi kotu ta hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu tsayawa takara a babban zaben 2027 saboda zargin ya gabatar da takardun karatu na bogi da kuma takardar NYSC ta karya.
Kungiyar ta yi zargin cewa takardun da aka gabatar wa INEC a lokacin zaben 2023 ba ingantattun takardu ba ne, tana mai neman kotu ta dauki matakin da zai hana shugaban kasar shiga zaben 2027.
Asali: Legit.ng
