Shugaban Musulmi na Duniya Ya Gana da Bola Tinubu a Abuja

Shugaban Musulmi na Duniya Ya Gana da Bola Tinubu a Abuja

  • Shugaban Kungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammed Al-Issa, ya gana da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja
  • Al-Issa ya gode wa Tinubu kan goyon bayan da ya bayar wajen ƙaddamar da shirin zaman lafiyar al'umma a Yammacin Afirka a Abuja
  • Sanarwar ta ƙunshi shirin haɗin gwiwar hukumomin gwamnati, shugabannin addinan Musulunci da Kiristanci da ƙungiyoyin farar hula domin ƙarfafa zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya, Mohammed Al-Issa, ya gana da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Al-Issa ya bayyana cewa ziyarar ta kasance wata dama ta nuna godiya ga Tinubu kan goyon bayan da ya bai wa shirin ƙarfafa zaman lafiya a Yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya tabo maganar raba Najeriya saboda sabani

Mohammed Al-Issa Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasashen Musulmi, Mohammed Al-Issa tare da Bola Tinubu. Hoto: Mohammed Al-Issa
Source: Facebook

Al-Issa ya yaba wa Tinubu

A sakon da ya wallafa a Facebook, Al-Issa ya ce ya ji daɗin ganawa da Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya nuna godiyarsa kan rawar da shugaban ya taka wajen ƙaddamar da shirin kungiyar.

Ya ce Tinubu ya kuma nuna cikakken goyon baya ga sakamakon taron, wato amincewa da sanarwar bayan taro da aka cimma a babban taron da aka gudanar a Abuja.

Abin da taron Abuja ya ƙunsa

Al-Issa ya bayyana cewa sanarwar ta ƙunshi tsarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati domin aiwatar da matakan da aka amince da su.

Haka kuma ta ƙunshi haɗin kai tsakanin shugabannin addinan Musulunci da Kiristanci tare da ƙungiyoyin farar hula.

An kuma amince da kafa wata hukuma ko ƙungiyar da za ta haɗa shugabannin addinai da na farar hula da cibiyoyi a Yammacin Afirka.

A gefe guda, an yarda cewa aikin ƙungiyar shi ne bibiyar yadda ake aiwatar da alkawuran da ke cikin tsarin haɗin gwiwar da aka amince da shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yayyafa ruwan sanyi bayan kalaman Jingir sun ta da kura

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Jakadan Saudiyya
Lokacin da jakadan Saudi a Najeriya ya gana da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jama'a sun yaba da shirin

Rashid Yahaya Numan ya bayyana amincewa da abin da ya kira wani babban ci gaba wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan al'umma.

Ya yaba wa JIBWIS da kungiyar bisa ƙoƙarin ƙarfafa zaman lafiya, fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da haɗin kan al'ummar Yammacin Afirka.

An nemi tallafin Saudiyya

Abubakar Alhaji Umar ya gode wa Al-Issa bisa ziyarar da ya kai Najeriya da kuma ƙoƙarin da ake yi wajen samar da zaman lafiya.

Ya nemi tallafin Masarautar Saudiyya ba kawai wajen gina masallatai ba, har da kafa masana'antu a Najeriya.

Ya ce hakan zai samar da guraben ayyukan yi, rage talauci da kuma taimaka wa Musulmi da sauran 'yan Najeriya samun halal ɗin abin dogaro da kai.

An yi taron zaman lafiya a Abuja

A wani labarin, mun ruwaito cewa an so Shugaba Bola Tinubu ya halarci babban taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da haɗin kan Najeriya da JIBWIS Nigeria ta shirya tare da haɗin gwiwar kungiyar Musulmai ta duniya.

Kara karanta wannan

Bayan haduwa da Tinubu, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya gana da Wike

Taron na kwanaki biyu ya mayar da hankali kan matsalolin garkuwa da mutane, 'yan bindiga da sauran ƙalubalen tsaro da ke addabar Najeriya.

An gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja, tare da halartar malamai, masu tsara manufofi, masana tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng