An Zabi Sabon Shugaban Majalisar Isra'ila, Netanyahu Ya Rasa Karfin Iko
- Majalisar dokokin Isra’ila ta zabi Matan Kahana a matsayin sabon shugabanta, matakin da ya kara raunana ikon Firaminista Benjamin Netanyahu a majalisa
- Kahana, dan jam’iyyar Yashar, ya samu kuri’un ’yan majalisa 66, yayin da dan takarar jam’iyyar Likud ta Netanyahu ya samu kuri’u 52
- Sabon zabin ya bai wa ‘yan adawa karin iko kan ayyukan majalisa, bayan kawancen Netanyahu ya rasa rinjayensa a zaben ranar 27 ga Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila – Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fuskanci sabon koma baya a siyasa bayan majalisar dokokin kasar ta zabi sabon shugaba, lamarin da ya bai wa ‘yan adawa karin iko kan ayyukan majalisar.
Majalisar dokokin Isra’ila, wato Knesset, ta zabi Matan Kahana na jam’iyyar Yashar ta Gadi Eisenkot a matsayin shugabanta na 26, inda ya maye gurbin Amir Ohana na jam’iyyar Likud ta Netanyahu.

Source: Getty Images
Rahoton da tashar CNN ta wallafa ya nuna cewa kakakin majalisar ya tabbatar da cewa Kahana ya samu goyon bayan ‘yan majalisa 66.
Benjamin Netanyahu ya rasa rinjaye a majalisa
Rahoto ya nuna cewa an gudanar da kada kuri’ar ne daban-daban ga ‘yan takarar biyu, ba tare da fafatawa kai tsaye a kuri’a guda ba.
Ofir Katz, wanda jam’iyyar Likud ta tsayar kuma mai kula da harkokin ‘yan majalisa na kawancen gwamnati, ya samu kuri’u 52.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Netanyahu da kawancen jam’iyyun masu ra’ayin dama da na addinin Yahudawa masu tsaurin ra’ayi sun kasa samun rinjaye a zaben majalisa na ranar 27 ga Oktoba.
Kawancen Netanyahu ya samu kujeru 53 ne kacal cikin kujeru 120 na majalisar, yayin da ‘yan adawa suka samu 67.
Daga cikin kujerun ‘yan adawa, jam’iyyun Yahudawa hudu sun samu 48, yayin da jam’iyyun Larabawa biyu, Joint List da Raam, suka samu jimillar kujeru 19.
Eisenkot na shirin kafa gwamnati
Gadi Eisenkot, wanda Shugaba Isaac Herzog ya daurawa alhakin kokarin kafa sabuwar gwamnati a farkon wannan watan, na da sauran makonni hudu da rabi domin kokarin maye gurbin Netanyahu.
Duk da haka, samun damar kafa gwamnati ba abu ne mai sauki ba, amma sabon zabin ya bai wa kawancen Eisenkot iko kan zaman majalisa, muhimman mukamai da kuma tsarin gabatar da kudurori.
Eisenkot ya ce zaben Kahana mataki ne na dimokuradiyya da ya dace, wanda ke nuna ra’ayin mafi yawan ‘yan majalisar da suka kada kuri’ar neman sauyi.

Source: Getty Images
The Guardian ta wallafa cewa kawancen ya kuma nada shugabannin rikon kwarya na wasu kwamitocin majalisa, ciki har da na harkokin kudi da tsaro.
Avigdor Liberman, shugaban jam’iyyar Yisrael Beitenu ta ‘yan adawa, wanda yanzu ke jagorantar kwamitin harkokin wajen Isra’ila da tsaro, ya ce zai gayyaci shugabannin hukumomin tsaro domin su yi wa kwamitin bayani.

Kara karanta wannan
Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki
Ahmed ya zama mataimakin Kahana
A wani labarin, mun rahoto cewa an nada dan majalisar Larabawa, Ahmed Tibi, a matsayin mataimakin shugaban majalisar dokokin Isra’ila, Knesset, matakin da ya zama wani gagarumin ci gaba ga wakilcin Larabawa a siyasar kasar.
Kwamitin tsara ayyukan majalisar ne ya amince da nadin nasa a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, tare da amincewa da wasu mataimakan shugabanni takwas na rikon kwarya.
Bayan nadin, Tibi ya bayyana cewa mukamin nasara ce da ta dace da Joint List, wadda ta samu kujeru 11 a zaben majalisar dokokin ranar 27 ga Oktoba.
Asali: Legit.ng

