Yakin Iran: Gwamnatin Amurka Ta Sake Hurawa Fafaroma Leo Wuta kan Trump
- Takaddama tsakanin Fafaroma Leo da gwamnatin Donald Trump na kara kamari bayan musayar yawu da suka yi kan yakin Iran da Amurka
- Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance ya bukaci Fafaroma Leo da ya kame bakinsa daga maganganun da suka shafi Trump
- A wani bangaren kuma, gwamnatin kasar Italiya ta caccaki Donald Trump kan maganganun da ya yi game da Fafaroma Leo a daren Lahadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya bukaci Fafaroma Leo ya mai da hankali kan harkokin addini maimakon wasu lamuran siyasa.
JD Vance ya bayyana haka ne yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Donald Trump da Fafaroma Leo kan yaƙin Iran da Amurka.

Source: Getty Images
Martanin JD Vance ga Fafaroma Leo
Shafin American Conservative ya wallafa bidiyon tambayoyin da aka yi wa JD Vance game da kalaman Fafaroma da amsar da ya bayar a kafar X.
Game da tsoma bakin Fafaroma kan lamuran Trump da gwamnatin Amurka, JD Vance ya ce:
“Tabbas ina ganin a wasu lokuta ya fi dacewa Vatican ta tsaya kan harkokin gyaran tarbiyya... sannan ta bar Shugaban Amurka ya tsara manufofin gwamnati,”
Kalaman mataimakin shugaban sun zo ne a daidai lokacin da Trump da Fafaroman, wanda haifaffen Amurka ne, ke ci gaba da musayar kalamai masu zafi kan rikicin Iran.
Ana cigaba da takaddama ne a lokacin da Trump ya ƙi ba da haƙuri bayan ya kira Fafaroma mai rauni kan fahimtar laifuffuka da kuma maras fahimtar harkokin ƙasashen waje.
Maganar shigar Trump a Yesu
JD Vance, wanda shi ma Kirista ne dan Darikar Katolika, ya kare wani hoton da Trump ya wallafa (wanda daga baya aka goge) a shafinsa na sada zumunta, inda aka nuna shi kamar Yesu Almasihu.
“Barkwanci shugaban yake yi,”
In ji Vance yayin kare shigar Trump a matsayin Yesu Almasihu
Italiya ta caccaki Trump kan Fafaroma
A wani ɓangaren, Firaministan Italiya, Giorgia Meloni, ta bayyana kalaman Trump kan Fafaroma Leo XIV a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.
BBC ta rahoto cewa Meloni ta ce:
“Fafaroma ne shugaban cocin Katolika, kuma daidai ne ya yi kira zuwa ga zaman lafiya tare da yin Allah-wadai da kowane irin yaƙi.”

Source: Getty Images
Meloni, wadda ita ma 'yar Darikar Katolika ce kuma ke jagorantar gwamnatin haɗin gwiwa a Italiya, na daga cikin na kusa da Trump, kuma a baya ba ta son sukar sa kan irin waɗannan kalamai.
Ga bayanin da JD Vance ya yi a bidiyo:
Fafaroma ya yi wa Trump raddi
A wani labarin, kun ji cewa Fafaroma Leo XVI ya shaida wa manema labarai yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Aljeriya cewa ba ya son shiga muhawara da Donald Trump.
Ya bayyana cewa ba ya jin tsoron gwamnatin Trump, kuma zai ci gaba da yin magana kan yaƙi bayan kalamai masu zafi da shugaban Amurka ya aika masa kan matsayarsa game da rikicin Iran.
Leo ya kasance mai sukar yaƙin Iran sosai, inda ya bayyana barazanar Amurka ta shafe Iran a doron kasa a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.
Asali: Legit.ng

