An Gano Wasu Mutanen da ke Rayuwa a Daji ba tare da Tufafi ba
- An gano wasu ’yan wata ƙabila da ta keɓe kanta daga sauran al’ummar duniya a cikin dajin Amazon da ke ƙasar Brazil
- Ƙungiyar kare haƙƙin ’yan asalin ƙasa ta ce masu sare itatuwa, mafarauta da masu kiwon shanu na ƙara jefa rayuwarsu cikin haɗari
- Hukumar kula da al’ummar ’yan asalin ƙasar Brazil ta ce ta fara ɗaukar matakan kare lafiyarsu bayan bayyanar hotunan ganawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Brazil – Wasu hotuna da ba kasafai ake ganin irinsu ba na wasu ’yan ƙabilar Awá da suka keɓe kansu daga sauran al’umma a dajin Amazon na ƙasar Brazil sun jawo hankalin masu rajin kare haƙƙin ’yan asalin ƙasa kan barazanar da suke fuskanta.
Ƙungiyar Survival International mai rajin kare haƙƙin ’yan asalin ƙasa da ke Birtaniya ce ta wallafa hotunan a ranar Talata, inda ta bayyana ganawar da aka yi da mutanen a matsayin lamari mai tarihi.

Source: Twitter
Yadda aka yi ganawar da ’yan ƙabilar
Reuter ta rahoto cewa kungiyar ta ce ganawar ta faru ne a ranar Litinin, lokacin da wasu jami’an gwamnati suka haɗu da kusan mutum 20 daga ƙabilar Awá a wani yanki mai nisa da ke jihar Maranhão, a Arewa maso gabashin Brazil.
An ce mutanen sun fito ne daga cikin dajin inda suka nemi abinci daga jami’an da suka haɗu da su.
Survival International ta bayyana cewa mutanen da suka keɓe kansu su ne waɗanda ke guje wa hulɗa da baƙi, kuma ba su da wata dangantaka ta dindindin da sauran al’umma, duk da cewa suna sane da abin da ke faruwa a wajen yankunansu.
Ƙungiyar ta wallafa a X cewa ba a samu irin wannan ganawa da ’yan ƙabilar Awá ba a cikin ’yan shekarun nan, musamman tun shekaru da dama da suka gabata.
Ga bidiyon mutanen da aka gani a kasa:
Barazanar da ke fuskantar ƙabilar Awá
Survival International ta yi zargin cewa matsin lambar da wasu mutane daga waje ke yi wa al’ummar ne ya sa suka fito neman abinci.
A cewar ƙungiyar, masu sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, mafarauta da masu kiwon shanu na kutsawa yankunan da ’yan ƙabilar suke zaune, lamarin da ke rage musu wuraren zama.
Daraktar ƙungiyar, Caroline Pearce, ta ce ’yan ƙabilar Awá na fuskantar matsananciyar barazana daga masu kutsawa yankunansu ta kowane bangare, har suna rasa wuraren zama a cikin dajin.
Ta ƙara da cewa hakan na tilasta musu zama a wani ƙaramin yanki na dajin Amazon da ke kewaye da wuraren da ake lalatawa.
Wani rahoto da BBC ta wallafa ya nuna cewa mutanen suna rayuwa ne a cikin daji ba tare da sanya tufafi ba.

Source: AFP
An kammala zaben Brazil
A wani labarin, mun rahoto cewa shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar, inda ya doke Sanata Flávio Bolsonaro mai alaƙa da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan
Yan takarar gwamnan ADC sun ɗauki zafi kan hukuncin hana Atiku takara a zaben 2027
Lula, mai shekaru 80, ya samu sama da kashi 51 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Bolsonaro ya ƙi amincewa da sakamakon zaɓen tare da bayyana cewa zai garzaya kotu domin ƙalubalantarsa.
Nasarar Lula ta zo ne bayan yaƙin neman zaɓe da aka fi mayar da hankali kan tsadar rayuwa, matsalar rashin tsaro da kuma cin hanci da rashawa a faɗin ƙasar Brazil.
Asali: Legit.ng

