Trump Ya Nanata Barazanar Kawar da Iran daga Doron Kasa, Ya Fadi Dalili

Trump Ya Nanata Barazanar Kawar da Iran daga Doron Kasa, Ya Fadi Dalili

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake gargadin Iran kan amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiyta a cikin gaggawa
  • Rahotanni sun ce shugaba Trump da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu sun tattauna kan rikicin Iran da yiwuwar sababbin hare-hare
  • Iran ta zargi Amurka da rashin sassauci a tattaunawar tsagaita wuta da kawo ƙarshen rikicin yayin da aka shafe watanni ana buga wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar USA - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake yin kakkausar barazana ga Iran, inda ya buƙace ta da ta gaggauta amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya kafin lokaci ya ƙure mata.

Trump ya bayyana haka ne bayan wata tattaunawa da ya yi da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kan cigaban rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila.

Kara karanta wannan

Rundunar tsaron Najeriya ta karyata bayanan Amurka kan kisan Abu Bilal Al Minuki

Amurka ta sake yi wa Iran barazana
Firaministan Iran, Masoud Pazeshkian da Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Masoud Pazeshkian/Donald J Trump
Source: Getty Images

BBC Hausa ta wallafa cewa shugabannin biyu sun tattauna kan yiwuwar komawa fagen yaƙi kai-tsaye, tare da yiwuwar kai sababbin hare-hare na haɗin gwiwa kan Iran.

Barazanar Donald Trump ga kasar Iran

Ita CNN ta ruwaito cewa sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Amurka ko Isra’ila da ta tabbatar da cewa an cimma matsaya kanshirin kai wa Iran sabon farmaki.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da fargaba a Gabas ta Tsakiya, yayin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin ganin an dakile rikicin kafin ya ƙara faɗaɗa.

Rahotanni sun bayyana cewa akwai fahimtar da ke ƙara ƙarfi a cikin Iran cewa ƙasar na ganin tana da ƙarfin jure matsin lambar da ake mata daga Amurka da Isra’ila.

Tun da farko, an samu rahotanni cewa Amurka ta gaza nuna sassauci a martanin da ta mayar kan buƙatun da Iran ta gabatar domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

"Ba tare da kashe kowa ba"; Obama ya fadi yadda ya kulla yarjejeniya da Iran

Rahoton ya ce rashin sassaucin gwamnatin Amurka na iya haddasa tsaiko a tattaunawar da ake yi domin kawo ƙarshen rikicin.

Trump ya magantu game da tsagaita wuta

Trump ya kuma sake jaddada barazanar da ya yi tun watan Afirilu kafin sanar da tsagaita wuta, inda ya ce Iran za ta fuskanci mummunan sakamako idan har ta ƙi amincewa da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

A farkon makon nan ma shugaban na Amurka ya bayyana cewa yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta tana cikin mawuyacin hali.

Shugaba Donald Trump ya bayyana haka ne bayan da ya yi watsi da wasu buƙatun gwamnatin Iran, yana mai cewa ba za a iya amincewa da su ba ko kaɗan.

An samu girgizar kasa a Iran

A baya, mun wallafa cewa an samu wata girgizar kasa mai karfin maki 4.6 kusa da birnin Pardis da ke gabashin Tehran a kasar Iran a daren Talata, 12 ga watan Mayun 2026.

Cibiyar kula da girgizar kasa ta Iran ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:16 na dare agogon GMT, inda aka ce girgizar ta faru a zurfin kilomita 10 a karkashin kasa.

Ya nuna cewa cibiyar girgizar kasar tana kusa da iyakar lardunan Tehran da Mazandaran, kimanin kilomita 41 daga birnin Tehran da kuma kilomita 77 daga Karaj.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng