Sabuwar Fitina: Trump Ya Tura Manyan Jiragen Yaki Kusa da Iran

Sabuwar Fitina: Trump Ya Tura Manyan Jiragen Yaki Kusa da Iran

  • Bayan tura jirage kusa da Iran, Amurka ta ce ta karkatar da jiragen ruwa na kasuwanci 55 a wani yunƙuri na aiwatar da takunkumin da ta kakaba wa Iran
  • Rundunar sojin ta ce an kuma hana wasu jiragen ruwa biyu aiki tare da shiga cikin wasu jirage biyu domin tabbatar da dokar takunkumin
  • Matakin ya zo ne yayin da har yanzu ake fuskantar rashin tabbas tsakanin Amurka da Iran bayan sake barkewar faɗa da kuma lalacewar yarjejeniyar diflomasiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

AbujaRundunar Sojin Amurka ta ce dakarunta sun karkatar da jiragen ruwa na kasuwanci 55 a wani yunƙuri na aiwatar da takunkumin da Washington ke jagoranta kan Iran.

Rundunar CENTCOM ce ta bayyana hakan, inda ta ce an kuma hana wasu jiragen ruwa biyu ci gaba da tafiya tare da shiga cikin wasu jiragen ruwa biyu yayin da sojojin Amurkan ke aiwatar da ayyukansu a yankin.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, an gano bindigogi 399 da aka yi shirin kawowa Najeriya

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na sauraron wani bayani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jiragen Amurka a kusa da Iran

ND TV ya wallafa cewa CENTCOM ta ce wasu sojojin ruwan Amurka suna aiki ne daga cikin jirgin ruwan USS Ross, wani babban jirgin yaƙi mai ɗauke da makamai masu linzami mai lamba DDG 71.

Jirgin na cikin sama da jiragen ruwan yaƙi 20 na Amurka da aka tura yankin Gabas ta Tsakiya domin gudanar da ayyuka daban-daban, ciki har da aiwatar da takunkumin da aka kakaba wa Iran.

Sai dai CENTCOM ba ta bayyana sunayen jiragen ruwan kasuwancin da aka karkatar ba, kuma ba ta yi cikakken bayani kan dalilan da suka sa aka ɗauki matakan da aka bayyana ba.

Rikici Amurka da Iran cigaba

Rahoton Yenisafak ya ce sababbin matakan na sojojin ruwan Amurka sun zo ne a lokacin da har yanzu ake fuskantar rashin tabbas tsakanin Washington da Tehran.

Rikicin ya fara ne a watan Fabrairu bayan Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da wani farmakin soji na haɗin gwiwa kan Iran.

Kara karanta wannan

An samu afkuwar ambaliya a Arewa, gidaje da wasu muhimman kadarori sun lalace

Lamarin ya janyo martanin hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami daga Iran kan ƙasashen Gulf da ke da sansanonin sojojin Amurka.

Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu, kafin daga bisani su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Pakistan ta shiga tsakani a watan Yuni.

Wasu jirage a hanyar mashigar Hormuz
Yadda jirage ke nufar hanyar Hormuz a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yunkurin diflomasiyya da ake yi

Sai dai yarjejeniyar watan Yuni ta rushe a watan da ya gabata, lamarin da ya haifar da kusan makonni biyu na sake barkewar hare-hare tsakanin Amurka da Iran.

Shugaban Amurka, Donald Trump, daga bisani ya bayar da umarnin dakatar da hare-haren bayan rahotannin da suka nuna cewa ana gudanar da wasu tattaunawar diflomasiyya domin shawo kan rikicin.

Shirin Trump kan yakin Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kasance a shirye ya kawo ƙarshen yaƙin da Iran ba tare da cimma yarjejeniyar nukiliya ba.

Trump ya tattauna hakan ne a asirce da manyan masu ba shi shawara, bayan shafe makonni yana shirin bayyana cewa Amurka ta yi nasara idan Iran ta bude Hormuz.

Sai dai wannan zaɓi ya ƙara fuskantar cikas bayan Iran ta buƙaci Amurka ta biya mata biliyoyin daloli, ta janye dakarunta daga yankin tare da kawo ƙarshen takunkumin sojin ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng