2027: Martanin Kwankwaso ga Zargin Yana Yi wa Tinubu Aiki a NDC

2027: Martanin Kwankwaso ga Zargin Yana Yi wa Tinubu Aiki a NDC

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce haɗakarsa da Peter Obi ba ta da alaƙa da addini ko yanki, illa ceto Najeriya
  • Ya bayyana cewa NDC na neman samar wa ‘yan Najeriya madadin shugabancin da ake da shi yanzu a kasar a yayin zaben 2027
  • Sanata Kwankwaso ya kuma tabo batun rikicinsa da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, inda ya bayyana cewa ya tafka babban kuskure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa alaƙarsa ta siyasa da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ta samo asali ne daga burin gyara Najeriya, ba wai saboda addini ko yanki ba.

Kara karanta wannan

"Babu irina": Peter Obi ya bayyana bambancinsa da Kwankwaso

Tsohon gwamnan wanda shi ma ya nemi takarar shugaban kasa a baya ya ce sbangarorin biyu sun fahimci cewa suna da manufofi iri ɗaya wajen samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya, musamman matasa.

Kwankwaso ya magantu kan taimakon Tinubu a 2027
Shugaba Bola Tinubu a gidan gwamnati da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso Hoto: @OfficialABAT, @RMKwankwaso
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata hira ta musamman da Trust TV, inda ya ce bayan tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, sun fahimci cewa dukkansu suna son ganin an inganta Najeriya.

Muna son inganta tsaro, cewar Kwankwaso

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce shi da Obi harkokin ilimi, tsaro, samar da ayyukan yi da kuma shugabanci nagari a ƙasar nan.

A cewarsa, wasu mutane suna ƙoƙarin ɗora haɗakar tasu a kan addini ko yanki, amma ya ce mafi yawan ‘yan Najeriya yanzu sun fi mayar da hankali kan shugabanci mai inganci da mafita ga matsin tattalin arziki.

Kwanlwaso ya ce son ceton Najeriya ne ya hada shi da Obi
Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso masu neman takara a zaben 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso ya kuma bayyana cewa jam’iyyarsu ta NDC tana ƙoƙarin zama wata sabuwar mafita ga ‘yan Najeriya kafin zaɓen 2027.

Ya ce:

“Mutane suna neman ilimi mai kyau, tsaro, ayyukan yi da zaman lafiya. Waɗannan su ne abubuwan da suka fi damun talakawan Najeriya yanzu.”

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito da korafe korafe kan Buhari game da taimaka masa a 2015

Kwankwaso ya musanta yi wa Tinubu aiki

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya kuma musanta zargin cewa yana aiki a ɓoye domin taimaka wa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓe a 2027.

Ya ce duk da irin surutan siyasa da ake yi, NDC na ƙara samun karɓuwa daga miliyoyin ‘yan Najeriya a cikin 'dan ƙanƙanin lokaci.

Kwankwaso ya kuma bayyana cewa babu wani lokaci da shi da Obi suka nemi tabbacin tikitin takarar shugaban ƙasa ko mataimaki kafin shiga tattaunawar haɗaka da jam’iyyu.

Da yake magana kan siyasar Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa rabuwar siyasarsa da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, babban kuskure ne ga gwamnan. Ya ce a tarihin siyasar Kano, duk wanda ya juya baya ga waɗanda suka taimaka masa hawa mulki ba ya ƙarewa da nasara. Sai dai ya jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya tana nan daram duk da sauya shekar wasu manyan ‘yan siyasa da ‘yan majalisa.

Martanin Kwankwasiyya ga PRP

Kara karanta wannan

Duk da yana NDC, Kwankwaso ya tabo batun aiki tare da Atiku, ADC a 2027

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmad ya yi zargin cewa Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso sun bukaci tikitin takarar shugaban kasa kafin shiga jam’iyyarsu.

Sai dai tuni kungiyar Kwankwasiyya ta musanta zargin, ta ce Baba-Ahmed na neman daukar hankali ne kawai amma ba gaskiya ya fada na cewa Kwankwaso da Obi sun nemi tikitin takara kai tsaye.

Kungiyar ta bayyana cewa PRP ce da kanta ta roki Kwankwaso da Obi su shigo jam'iyyar amma babu wani zama da aka yi kan wannan batu a lokacin da ake neman mafita bayan rikicin ADC ya zafafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng