Yahudawa Sun Bankawa Masallaci, Motoci Wuta yayin Ibada a Isra'ila
- Wasu ƴan Isra’ila sun kai hari a wani masallaci yayin da suka banka wuta kan motoci da ke harabar wurin ibadar
- Majiyoyi suka ce lamarin ya faru ne a kauyen Jibiya da ke kusa da Ramallah, tare da rubuta kalaman wariyar launin fata a bangon gidaje
- Maharan yahudawa sun kai hari gidajen Falasdinawa a Al-Lubban al-Sharqiya kusa da Nablus, inda suka karya kofofi da firgita mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Isra’ilawa sun kona wani masallaci da motoci mallakin Falasdinawa a safiyar Juma’a 15 ga watan Mayun 2026.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Yahudawan sun aikata hakan ne a kauyen Jibiya da ke arewa maso yammacin Ramallah.

Source: Facebook
Yahudawa sun kona masallaci a Isra'ila
Majiyoyi sun shaida wa Al Jazeera cewa maharan sun shiga kauyen, suka banka wa masallacin da motoci wuta tare da rubuta kalaman wariya.
Har ila yau, sojojin Isra’ila sun kutsa cikin birnin Nablus inda suka kai samame gidaje, lamarin da ya kai ga kama akalla mutum guda, cewar Anadolu Ajansi.
Wadannan sababbin hare-hare sun sake nuna irin tsananin tashin hankalin da ake fama da shi a yankin, yayin da mazauna ke fuskantar matsin lamba daga farmakin soji da kuma karuwar lalata kadarori da kungiyoyin matsugunan Yahudawa ke yi.
Yahudawa sun farmaki gidajen Faladinawa
A wani harin daban, Yahudawa sun kai farmaki gidajen Falasdinawa a garin Al-Lubban al-Sharqiya da ke kudancin Nablus a Yammacin Kogin Jordan.
Majiyoyin tsaro sun ce maharan sun lalata kofofin gidaje da ke kan babban titin garin, lamarin da ya jefa mata da yara cikin firgici.
Rahotanni sun nuna cewa Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus na fuskantar karin farmakin sojojin Isra’ila da kuma hare-haren yahudawan mamaya kan Falasdinawa.

Source: Getty Images
Falasdinu ta yi Allah-wadai da lamarin
Ma’aikatar kula da harkokin addini da wakafi ta Falasdinu ta yi Allah-wadai da kona wani masallaci da kuma wasu motocin fararen hula.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da WAFA News Agency ta samu, ma’aikatar ta ce harin ba wani lamari ne na daban ba, illa wani bangare na tsari da kuma tunzurin hukuma daga gwamnatin Isra’ila domin tsoratar da Falasdinawa.

Kara karanta wannan
Hajjin 2026: Kasar Saudiyya ta yi gyare gyare, ta tura tallafi ga kasashen Musulmi 27
Ma’aikatar ta bayyana kona masallatai a matsayin “aikin ta’addanci na matsorata” wanda ke nuna “matsananciyar akida da ba ta mutunta addinai ko dokokin kasa da kasa.”
Ta kara da cewa shirun da kasashen duniya suka yi kan hare-haren da ake ci gaba da kai wa wuraren ibada na Musulmi da Kiristoci yana karfafa lamarin.
An kashe sojan Isra'ila a Lebanon
Mun ba ku labarin cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa mayakan kungiyar Hezbollah sun harba makamai kan rukunin sojojin Isra'ila da ke a Kudancin kasar Lebanon.
Daya daga cikin makamin ya fashe a kusa da wani sojan Isra'ila, wanda ya bar duniya duk da kokarin ceto shi da aka yi.
Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa sojan ya mutu ne yayin fafatawa a Kudancin Lebanon, ana ci gaba da musayar hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Asali: Legit.ng
