Hajjin Bana: Wata Maniyyaciya daga Najeriya Ta Rasu Awanni da Isa Saudiyya

Hajjin Bana: Wata Maniyyaciya daga Najeriya Ta Rasu Awanni da Isa Saudiyya

  • Wata maniyyaciya ƴar shekara 73 daga Jihar Adamawa, Mallama Aishatu Muhammadu, ta rasu a hanyarta ta zuwa Madina
  • Hukumar NAHCON ta bayyana cewa ciwon zuciya ne ya yi sanadin mutuwar tata yayin da take cikin tafiya daga birnin Jeddah
  • Shugaban NAHCON ya jajantawa iyalan mamaciyar tare da ba su tabbacin dawo musu da dukkan kayayyakin da ta bari a ƙasa mai tsarki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Saudiyya - Najeriya ta yi rashin wata maniyyaciya ƴar shekara 73 daga Jihar Adamawa, Mallama Aishatu Muhammadu.

Malama Aishatu ta rasu a ranar Asabar, awanni da isa Jeddah, yayin da take shirin gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Wata maniyyaciya daga Adamawa ta rasu a hanyar zuwa Jeddah yayin shirin fara Hajjin 2026
Wasu mahajjata daga Najeriya sun isa Saudiyya. Hoto: @HajjReportersNG
Source: Twitter

Maniyyar Adamawa ta rasu a Saudiyya

Hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya (NAHCON) ce ta sanar da rasuwar maniyyaciyar a sanarwar da ta wallafa a shafinta na X a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

"Da hannun Tinubu": ADC ta yi fallasa kan 'dalilin' farfado da NDC

Sanarwar ta nuna cewa maniyyaciyar ta gamu da bugun zuciya ne ba tsammani yayin da take kan hanya daga Jeddah zuwa birnin Madina mai tsarki, abin da ya zamo ajalinta.

Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya isar da saƙon ta'aziyyar gwamnatin tarayya ga iyalan marigayiya Mallama Aishatu, wadda ta fito daga ƙaramar hukumar Gombi a Jihar Adamawa.

Sanarwar NAHCON ta ce:

"Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya mika sakon ta'aziyya a madadin gwamnatin tarayya ga iyalan Mallama Aishatu Muhammadu, maniyyaciya daga ƙaramar hukumar Gombi a Jihar Adamawa da ta rasu a Saudiyya a ranar 9 ga watan Mayun 2026, tana da shekaru 73.
"Maniyyaciyar ta rasu ne a sakamakon bugun zuciya yayin da take kan hanya daga Jeddah zuwa birnin Madina."

NAHCON ta yi waya da iyalan maniyyaciyar

Yayin wata tattaunawa ta wayar taraho da ɗan uwan mamaciyar, Umaru Jauro Koko, Ambasada Yusuf ya yi addu'ar Allah ya jiƙan marigayiyar da gafararsa tare da ba ta masauki a gidan Aljanna.

Ya bayyana cewa mutuwa a kan hanyar ibada babban rabo ne, amma rashi ne mai raɗaɗi ga iyali da kuma ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Najeriya da Moroko sun kulla sabuwar yarjejeniya, ta shafi manyan bangarori 3

Haka kuma, shugaban na NAHCON ya ba wa iyalan mamaciyar tabbacin cewa gwamnati za ta ba su dukkan goyon bayan da ya dace.

Wannan ya haɗa da tabbatar da cewa dukkan kayayyakin marigayiyar, da kuɗaɗen alawus ɗinta (BTA), da kuma takardar shaidar mutuwarta sun isa hannun iyalinta ta hanyar hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Adamawa.

A ranar 9 ga Mayun 2026 ne aka fara jigilar maniyyata aikin Hajjin Adamawa zuwa Saudiyya.
Wasu daga cikin maniyyatan Adamawa a kasa mai tsarki. Hoto: Mikail Danjuma Mub
Source: Facebook

Zuriyar da maniyyaciyar ta bari

Marigayiya Mallama Aishatu ta bar ƴaƴa da jikoki da kuma tattaba-kunne da dama a duniya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Daga cikin ƴaƴan nata, akwai babban jami'in rundunar tsaro ta NSCDC mai kula da shiyyar Ganye (D.O) da ke Jihar Adamawa.

Wannan rashi dai ya zo ne a daidai lokacin da maniyyata daga sassan Najeriya ke ci gaba da isa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.

Karanta sanarwar a nan kasa:

An fara jigilar maniyyatan Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, NAHCON ta fara jigilar maniyyatan Hajjin 2026 da maniyyata 474 daga Kogi, yayin da manyan jami’ai suka halarci bikin ƙaddamarwar a Abuja.

Kara karanta wannan

SDP 2027: Jam'iyyar adawa ta farko ta tsaida ɗan takarar shugaban kasa

Shugaban NAHCON, Ismail Abba Yusuf, ya bukaci maniyyata su bi dokokin Saudiyya tare da amfani da katin Nusuk domin tabbatar da sauƙin zirga-zirga da tsaro.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da gwamna Ahmed Ododo sun roki maniyyata su wakilci Najeriya cikin mutunci, addu’a, zaman lafiya da biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com