Dan Damfara Ya Sace wa Mahajjaciya 'Yar Najeriya Daloli a Madina

Dan Damfara Ya Sace wa Mahajjaciya 'Yar Najeriya Daloli a Madina

  • Rahotanni sun nuna cewa wata mahajjaciya ‘yar asalin Najeriya ta fada hannun wasu 'yan damfara a birnin Madina na kasar Saudiyya
  • Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an damfari matar ne bayan da aka yaudare ta aka canza mata kudin guzirin ta na aikin Hajji
  • A bayanin da majajjaciyar ta yi wa manema labarai, ta ce wani mutum ya karɓe mata Dalar Amurka da yawa sannan suka bata Dala 5 kacal

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Duk da gargadin da hukumar alhzai ta kasa (NAHCON) ke yi na cewa ya kamata mahajjata su yi taka tsan-tsan, an damfari wata mata a Madina.

Wani rahoto ya nuna cewa duk da matakan da hukumomi ke dauka, 'yan damfara na cigaba da fito da hanyoyin cutar mahajjata daga kasashe da dama.

Kara karanta wannan

Takara: Kalaman Pantami sun tayar da kura, an shawarce shi kan zaman lafiya

Maniyyata na shirin tafiya kasar Saudiyya
Yadda mahajjata ke shiga jirgi domin tafiya Saudiyya a Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Hukumar Alhazai ta kasa ta wallafa bidiyon tattaunawar da wani dan jarida ya yi da matar da aka damfara makudan kudi a Madina a shafinta na X.

'Yar Najeriya da aka damfara

A wata tattaunawa da aka yi da matar ta bayyana cewa mutumin ya zo ya same ta ya ce mata an raba tallafin kudin gwamnati amma ita ba ta samu ba.

Ta ce ta fito daga masallaci ne bayan sallah sai mutumin ya ce mata ana raba tallafin kudi a Saudiyya kamar yadda aka raba musu a Najeriya.

Yayin da ta nuna kamar ba ta yarda ba, sai ya nuna mata ran shi ya baci, inda ya ce yana kokarin taimakonta amma tana wasa da lamarin.

"E, ya ce ga gwambati ta turo da tallafi amma ke baki karba ba, ki zo na kai ki ki karba.
'Ya ce min Hajiya, ga shi mun kai mata sun karba ke ba ki nan, zo mu je ki karba. Sai ya ce in nuna masa kudin aka ba ni a Najeriya,

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru, an haramta wa masu digirin girmamawa amfani da 'Dr' a Najeriya

"sai ya ce akwai wani abu a jakar kudin ki? To kamar shi za a baki.

Da ta nuna shakku sai ya ce:

"Ina miki magana ke kina mayar da magana ta banza, kawo in ga rubutun da ke cikin jakar kudin ki, sai na ce ya ba ni kudi na, sai ya sauya min jakar."
Mahajjatan Najeriya a Saudiyya
Yadda wasu 'yan Najeriya suka isa kasar Saudiyya domin aikin Hajji. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Adadin kudin da aka sace mata

Hukumar NAHCON ta sanar da cewa a jakar kudin matar da ya karba ya sace mata Dala 55, inda ya mayar mata da Dala 5 kacal a lokacin da ta nemi ya ba ta kudinta.

Matar ta ce ta gano ya rage mata kudin ne a lokacin da ta ga mata 'yan uwanta na kirga kudin da suke da shi amma taga nata ya dawo kadan.

NAHCON ta gargadi mahajjata da su yi taka tsantsan wajen canjin kudi ko makamancin haka ba tare da tantance wanda za su yi alaka da shi ba.

Ga bayanin da matar ta yi a bidiyo:

Kara karanta wannan

Bidiyo: Zanga zanga ta barke bayan shiga asibiti a kama dan Najeriya a Amurka

'Yar Najeriya ta rasu a Saudi

A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da rasuwar wata mata 'yar jihar Adamawa.

An sanar da cewa matar mai suna Aishatu Muhammadu ta rasu ne a hanyar zuwa birnin Madina jim kadan bayan sauka a kasar Saudiyya.

Hukumar ta sanar da cewa ciwon zuciya ne ya yi sanadiyar rasuwar Aishatu Muhammad, inda ta yi wa 'yan uwanta ta'aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng