A Wata ga Wata: Trump zai Tunkari Iran da Dakaru, zai Tura Sojoji Hormuz

A Wata ga Wata: Trump zai Tunkari Iran da Dakaru, zai Tura Sojoji Hormuz

  • Ana cigaba da takaddama tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya musamman yayin da aka gaza cimma matsaya kan mashigar Hormuz
  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce kasar shi za ta taimaka wajen fitar da jiragen ruwa da suka makale daga mashigar da Iran ta toshe
  • Iran ta toshe mashigar Hormuz ne tun bayan harin da Amurka/Isra'ila suka hada kai suka kai mata a karshen watan Fabrairun shekarar 2026

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Gwamnatin Amurka ta fara shirin kutsawa mashigar Hormuz da Iran ta toshe domin hana jiragen ruwa wucewa zuwa kasashe.

An tattauna tsakanin Amurka da Iran a Pakistan domin tsayar da yaki gaba daya da bude mashigar amma har yanzu ba a cimma matsaya ba.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump da mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Trump zai tura sojoji Hormuz

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta canza shawara kan batun sulhu da Amurka, ta miika sabon tayi

BBC ta wallafa cewa shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka za ta taimaka wajen jagorantar jiragen ruwa da suka makale domin su fita daga mashigar ruwan Hormuz daga yau Litinin.

“Domin Iran, Gabas ta Tsakiya, da Amurka, mun sanar da wadannan kasashe cewa za mu taimaka wajen jagorantar jiragensu cikin aminci daga wadannan hanyoyin ruwa da aka toshe,”

In ji Trump, ba tare da bayyana kasashen da za su amfana ba.

Rahoton AP ya nuna cewa Trump ya ce duk wani yunkurin kawo cikas ga wannan aiki, wanda ya kira “Na samar da 'yanci”, za a “tunkare shi da karfi”.

Amurka na tattaunawa da Iran

A sakon Trump, ya ce wakilan Amurka na gudanar da tattaunawa mai kyau sosai da Iran, kuma wadannan tattaunawar na iya haifar da wani abu mai kyau ga duniya.

Trump ya kara da cewa tura sojoji Hormuz aikin jin kai ne da ake yi a madadin Amurka, Iran da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya, ba tare da lissafa wadannan kasashe ba.

Hedikwatar rundunar Amurka ta ce ma’aikata 15,000, jiragen ruwan yaki masu makamai masu linzami, da jiragen sama sama da 100 za su shiga cikin sabon shirin da Trump ya kawo game da mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Shirin dawowa yaki: Kasar Iran za ta kai dogayen hare hare kan Amurka

Yadda mashigar Hormuz da ke Iran ya ke
Mashigar Hormuz da ake rikici a kansa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kiyasta cewa kusan matukan jiragen ruwa 20,000 sun makale a Tekun Fasha tun bayan fara yakin da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan Iran.

An nuna damuwa kan karancin kayayyaki da kuma tasirin da hakan ke yi ga lafiyar jiki da kwakwalwa na ma’aikatan jiragen da ma sauran kasashe a fadin duniya.

Iran ta yi wa Amurka barazana

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin Iran ta yi gargadin kai manyan hare-hare kan kadarorin Amurka da kawayenta a Gabas ta Tsakiya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara rade-radin cewa Isra'ila da Amurka sun fara shirin cigaba da yaki da Iran bayan tsagaita wuta.

Wani babban sojan Iran ya sanar da cewa idan Amurka ta kuskura ta kai mata hari, Tehran za ta yi martani mai radadi da ba zai mata dadi ba sam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng