Iran Ta kai Farmaki kan Jirgin Ruwan Amurka a Kusa da Mashigar Hormuz

Iran Ta kai Farmaki kan Jirgin Ruwan Amurka a Kusa da Mashigar Hormuz

  • An ruwaito cewa makamai masu linzami biyu sun bugi wani jirgin ruwan yaki na kasar Amurka kusa da Jask a mashigar ruwa ta Hormuz
  • An bayyana cewa hakan ta faru ne bayan Amurka ta ya yi watsi da gargadin rundunar sojin Iran da ta bukaci ya jirgin ruwan ya tsaya
  • Rahoton harin ya biyo bayan sanarwar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi game da shirinsa na raka jiragen ruwa su wuce ta Hormuz

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kasar Iran ta ce ta tilasta wani jirgin yaki na Amurka ya juya baya daga shiga mashigar Hormuz a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Sai dai wani jami’in Amurka ya musanta rahoton cewa an harbe shi da makamai masu linzami na Iran, kamar yadda wasu bayanai suka nuna.

Kara karanta wannan

Lamari zai dagule: Iran ta ja kunnen Trump game da tura sojoji Hormuz

Jirgin ruwan Amurka a teku
Wani jirgin ruwa da aka kai wa hari a teku. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasar Iran ta farmaki jirgin Amurka

Al Jazeera ta wallafa cewa rundunar ruwan Iran ta ce ta hana jiragen yaki na Amurka da Isra'ila shiga yankin mashigar Hormuz ta hanyar gargadin gaggawa.

Wasu rahotanni daga Iran sun bayyana cewa makamai masu linzami biyu sun bugi jirgin yakin Amurka kusa da tashar Jask a bakin mashigar.

Takaddama kan mashigar Hormuz

Iran ta gargadi sojojin Amurka a ranar Litinin da kada su shiga wannan muhimmiyar mashigar ruwa bayan Trump ya ce Amurka za ta jagoranci fitar da jiragen ruwa da suka makale.

Trump bai bayar da cikakkun bayanai ba kan yadda za a taimaka wa jiragen da ma’aikatansu da suka makale a mashiga mai muhimmancin ba, inda suke fama da karancin abinci da sauran kayayyaki bayan fiye da watanni biyu na rikici.

A martani, rundunar hadin gwiwa ta Iran ta gargadi jiragen kasuwanci da tankokin mai da su guji duk wani motsi da bai samu amincewar sojojin Tehran ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Trump tunkari Iran da dakaru, zai tura sojoji Hormuz

“Mun sha bayyana cewa tsaron mashigar Hormuz yana hannunmu, kuma dole zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasance cikin hadin gwiwa da rundunar sojin mu,”

In ji Ali Abdollahi, shugaban rundunar hadin gwiwar Iran.

Martanin Amurka ga ikirarin Sojojin Iran

Bayan sanarwar da Iran ta fitar, hedikwatar rundunar Amurka ta ce babu wani jirgin ruwan ta da aka kai wa hari a mashigar Hormuz.

“Dakarun Amurka na tallafawa aikin da 'yan uwansu ke yi, kuma suna aiwatar da toshe hanyoyin ruwa a kan tashoshin jiragen Iran,”

In ji ta a shafin X.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na bayani a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar ta saba da rahoton farko da ya fito daga Tehran da ya ce makamai masu linzami biyu sun bugi wani jirgin ruwan Amurka kusa da Jask bayan ya ki bin umarnin rundunar ruwan Iran na tsayawa.

Iran ta gargadi Trump kan Hormuz

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Iran ta gargadi Shugaban Amurka, Donald Trump kan cewa zai tsoma baki a mashigar Hormuz.

Iran ta ce katsalandan din Amurka a tsarin zirga-zirgar a mashigar Hormuz zai kasance karya yarjejeniyar tsagaita wuta kuma ba za a yarda da shi ba.

Wani babban jami'in Iran ya bayyana cewa dukkan sakonnin da Trump ke wallafawa a kafafen sadarwa ba za su taimaka wajen bude Hormuz ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng