Yadda Barazanar Iran Ta Firgita Trump, Ya Sauya Jirgi kan Tsoron Kashe Shi

Yadda Barazanar Iran Ta Firgita Trump, Ya Sauya Jirgi kan Tsoron Kashe Shi

  • Barazanar kashe Shugaban Amurka, Donald Trump, daga Iran ta sa an gudanar da wani shiri na musamman domin ɓoye jirgin da ya ɗauke shi daga Turkiyya
  • An sauya Trump daga tsohon jirgin Air Force One zuwa ƙaramin jirgin soja na C-32A ba tare da sanin manema labarai da wasu ma'aikata ba
  • Rahoton da aka fitar ya ce an yi hakan ne saboda barazanar harin makami mai linzami daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC – Barazanar kashe Shugaban Amurka, Donald Trump, da ake zargin ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran ne suka shirya, ta sa aka gudanar da wani gagarumin shiri na sirri domin tsaron shugaban.

Hakan na zuwa ne yayin da kasashen ke cigaba da sabani da juna bayan gwabza yakin da suka yi na watanni a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yadda Trump ya tsara 'guduwa' daga yakin da ya ke da Iran

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump zai shiga jirgi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Washington Post ya ce an gudanar da shirin ne ranar 8 ga Yulin 2026, lokacin da Trump ke barin Turkiyya bayan halartar taron NATO a Ankara.

Yadda aka ɓoye tafiyar Trump

Rahoton ya ce Trump ya isa Turkiyya ne da sabon jirgin Boeing 747-8 da Qatar ta bai wa Amurka kyauta.

Amma saboda wata barazana da jami'an Amurka suka ɗauka da muhimmanci, musamman yiwuwar kai wa jirgin hari da makami mai linzami, an shirya sauya jirgin da zai ɗauki Trump.

An nuna Trump yana shiga tsohon jirgin Air Force One a gaban kyamarorin manema labarai, amma bayan mintuna kaɗan aka fitar da shi a ɓoye.

An yi amfani da wata motar jigilar abinci a filin jirgin sama wajen kai Trump daga ɗayan gefen jirgin zuwa wani jirgin soja kirar C-32A.

Jirgin C-32A ƙaramin jirgin soja ne da aka sauya daga Boeing 757 domin amfani da manyan jami'an gwamnatin Amurka.

Kara karanta wannan

Wuta ta yi wuta: Babban sojan Amurka na neman a fita a yaki da Iran

An kawar da hanklin jama'a

Wasu 'yan jarida da ma'aikatan Fadar White House sun shiga tsohon Air Force One suna zaton Trump na cikin jirgin.

An kuma umarce su da su rufe labulen tagogin jirgin, yayin da aka yi amfani da shi a matsayin jirgin basaja domin ɓoye ainihin jirgin da Trump ke ciki.

Rahoton Roya News ya nuna cewa ministan yakin Amurka, Pete Hegseth, shi ma ya shiga jirgin C-32A ta wata hanya dabam.

Shugaba Donald Trump a Amurka
Donald Trump na yi wa Amurkawa jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun kawo ƙarshen yaƙin Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya kasance a shirye ya kawo ƙarshen yaƙin Iran ba tare da samun yarjejeniyar nukiliya ba, muddin Tehran ta sake buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya.

Rahoto ya ce Trump ya yi wannan tunanin a sirrance tare da manyan mashawartansa, bayan makonni ana shirin bayyana nasarar Amurka idan Iran ta dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin walwala a mashigar.

Sai dai shirin ya ƙara fuskantar cikas bayan Iran ta buƙaci a biya ta biliyoyin daloli, a janye sojojin Amurka daga yankin tare da kawo ƙarshen shingen ruwan da Amurka ta kafa, da wasu sharuda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng