Shugaba Paul Biya na Kamaru Ya Yi Batan Dabo, Wata 2 ba a Gan Shi ba

Shugaba Paul Biya na Kamaru Ya Yi Batan Dabo, Wata 2 ba a Gan Shi ba

  • Shugaban Kamaru, Paul Biya, mai shekaru 93, ya shafe kusan watanni biyu a Turai bayan ya bar ƙasar domin abin da fadar shugaban ƙasar ta bayyana a matsayin “ɗan gajeren hutu”
  • Biya ya bar Kamaru ranar 7 ga Yunin 2026, kuma rashin dawowarsa ya sake haifar da tambayoyi kan lafiyarsa da kuma yadda ake tafiyar da gwamnati yayin da yake wajen ƙasar.
  • A shekarar 2025, Biya ya lashe wa’adin mulki na takwas a zaɓen da abokan hamayyarsa suka ce an tafka magudi, wanda kuma ya kasance tare da arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yaoundé – Shugaban Kamaru Paul Biya ya kwashe watanni biyu ba tare da dawowa ƙasar ba bayan tafiyarsa zuwa Turai a ranar 7 ga Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Fadar shugaban ƙasar ta ce ya tafi ne domin “ɗan gajeren hutu”, amma tsawon lokacin da ya yi a wajen ƙasar ya zama ɗaya daga cikin mafi tsawo da ya yi ba tare da dawowa ba cikin ‘yan shekarun nan.

Shugaban kasa Paul Biya
Paul Biya na sauraron jawabi a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

An ce Biya na Geneva

CNN ta wallafa cewa a makon da ya gabata, Kakakin gwamnatin Kamaru, René Emmanuel Sadi, ya tabbatar wa 'yan jarida cewa Biya yana Geneva, Switzerland.

Sadi ya musanta cewa shugaban yana kwance a asibiti, amma bai yi ƙarin bayani kan inda yake zaune ko lokacin da zai dawo Kamaru ba.

Rashin dawowar shugaban ya sake farfado da ce-ce-ku-ce kan lafiyarsa da kuma wanda ke gudanar da harkokin ƙasar a lokacin da yake wajen Kamaru.

Shugaban kasar Kamaru
Paul Biya a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Biya ya shafe shekaru 44 a mulki

Biya ya zama shugaban Kamaru a shekarar 1982 bayan ya karɓi ragamar mulki sakamakon murabus ɗin shugaban ƙasar na lokacin.

Financial Afrik ta wallafa cewa a shekarar 1984 ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na farko, sannan ya ci gaba da lashe wasu zaɓuka shida bayan ƙasar ta koma tsarin jam’iyyu da dama.

A shekarar 2025 ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya samu wa’adin mulki na takwas wanda zai iya sanya shi ci gaba da mulki har ya kusa shekara 100.

Kara karanta wannan

'Don Allah, a bari mu sarara': Kwankwaso ya 'gano' shirin Tinubu kan zaben 2027

Ana tambayar lafiyar Paul Biya

Biya ya shafe dogon lokaci yana yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje tun bayan da ya zama shugaban Kamaru, yayin da ba kasafai ake ganinsa a bainar jama’a ba.

Jita-jitar rashin lafiyarsa da inda yake zama ta dade tana yawo a Kamaru, lamarin da ya sa ofishinsa ke yawan musanta rahotannin cewa yana fama da mummunar rashin lafiya ko kuma ya mutu.

A shekarar 2024, gwamnatin Kamaru ta haramta wa kafafen yaɗa labarai tattauna lafiyar shugaban, tana mai bayyana batun a matsayin lamari da ya shafi tsaron ƙasa.

Iran ta zargi Faransa da munafurci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Iran ta zargi Faransa da wasu ƙasashen Yamma da munafurci bayan Tarayyar Turai da wasu ƙasashe 26 suka yi Allah-wadai da kisan masu zanga-zanga da gwamnatin Iran ta aiwatar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce sanarwar ƙasashen Yamma wani yunƙuri ne na kauce wa alhakin abin da Tehran ta kira manyan take hakkin bil’adama da dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, shi ma ya zargi Faransa da zama mai fuska biyu kan yadda take magana game da haƙƙin bil’adama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng