Abin da Zai Faru idan Amurka Ta Taimakawa Isra'ila wajen Kai wa Iran Hari

Abin da Zai Faru idan Amurka Ta Taimakawa Isra'ila wajen Kai wa Iran Hari

  • Shugaba Donald Trump na nazarin taimakawa Isra'ila kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, yayin da ya yi barazana ga Ali Khamenei
  • Ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta ce wannan ba yaƙin Amurka ba, don haka bai kamata Trump ya ce zai shigar wa ƙasar Isra'ila fada ba
  • Iran ta yi gargadin cewa idan har Amurka ta kuskura ta taimakawa Isra'ila, to kuwa balbalin bala'i ne zai sauka a Gabas ta Tsakiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - Shugaban Amurka, Donald Trump, yana nazarin ko zai taimakawa Isra'ila wajen kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Amurka na iya amfani da manyan makamai don kai hari a Fordo, wani muhimmin wurin nukiliyar ƙarƙashin ƙasa na Iran.

Iran ta ce idan Amurka ta shigarwa Isra'ila a fadan da suke yi, to Gabas ta Tsakiya ta shiga cikin masifa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump | Babban jagoran kasar Iran, Ali Khamenei | Getty Images
Asali: Getty Images

Trump ya yi barazana ga shugaban Iran

BBC ta ruwaito cewa shugaban Amurka ya gana da tawagarsa ta tsaron ƙasa a ranar Talata don tattauna matakai na gaba kan shiga rikicin Iran da Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manazarta sun ce kalaman Trump na nuna shirinsa na taimakawa Isra'ila, duk da kiran da ya yi a baya na tsagaita wuta da kuma goyon bayansa ga sulhu ta hanyar diflomasiyya.

An ce Trump na ci gaba da nuna takaici game da rashin samun ci gaba wajen tabbatar da sabuwar yarjejeniya da za ta yi hana Iran ƙera makamin nukiliya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Trump ya yi barazana ga babban jagoran Iran, Ali Khamenei, kuma ya ce Amurka ta san inda yake.

"A yanzu ba za mu kashe shi ba. Amma ba ma son a harba makamai masu linzami kan fararen hula, ko sojojin Amurka. Haƙurinmu ya kusa ƙarewa."

- Shugaba Donald Trump.

'Wannan ba yaƙin Amurka ba ne' – Khatibzadeh

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya maimaita cewa Iran tana a shirye domin sasanta komai ta hanyar diflomasiyya.

Amma Khatibzadeh ya sake jaddada cewa yayin da hare-hare kan ƙasarsa ke ci gaba, "babu wanda zai iya yin maganar sulhu a yanzu."

Ya ƙara da cewa:

"Da zarar wannan zaluncin ya tsaya, ba shakka diflomasiyya ita ce zaɓi na farko da Iran za ta kalla."

Ya jaddada cewa:

"Wannan ba yaƙin Amurka ba ne, kuma idan Trump ya shiga, to har abada za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin shugaban da ya shiga yaƙin da bai shafe shi ba.
"Muna ganin cewa wannan yaƙin ba yaƙin Amurka ba ne. Shigar Trump yaƙin nan zai zama tashin tashina mai girma, kuma zai zama bala'i mai girma ga dukkanin yankin."
Iran ta gargadi Trump kan shiga fadanta da Isra'ila, tana mai cewa yakin bai shafi Amurka ba
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump | Mataimakin minstan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Za mu ci gaba da kare kanmu' – Khatibzadeh

Khatibzadeh ya ƙara da cewa suna samun "saƙonni ta bayan gida" daga Amurka, kan cewa Washington ba ta da hannu a harin Isra'ila kuma ba za ta shiga ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko akwai hanyar kawo ƙarshen yaƙin, ya ce Iran tana kare kanta ne a yanzu bayan an kai mata hari da farko, inda daruruwan fararen hula 'yan Iran suka mutu.

"Muna kan kare kamu ne a yanzu, kuma za mu ci gaba da wannan kare kan har sai mai cin zarafin ya ɗauki darasi cewa ba zai iya kai harin zalunci a kan mu, mu kyale ba."

- Saeed Khatibzadeh.

'Trump ya rura rikicin Iran-Isra'ila' - China

A wani labarin, mun ruwaito cewa, China ta zargi tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, da “rura wutar rikici” tsakanin Iran da Isra’ila, biyo bayan gargadinsa na kwashe jama’ar Tehran.

Isra’ila ta kai farmaki kan wuraren Iran don dakile shirinta na nukiliya, lamarin da ya tayar da ƙararrawar yiwuwar rikicin yaƙi ya bazu a Gabas ta Tsakiya.

China ta kuma bukaci 'yan ƙasarta da su fice daga Isra’ila, ganin yadda rikicin ke kara tsananta, tare da lalata ababen more rayuwa da hallaka rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.