Bidiyo: Mimbarin Siyasa Ya Ruguzo Kasa Gwamna na tsaka da Bayani a Kamfe
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, da wasu jagororin jam’iyyar Accord sun tsallake rijiya da baya a ranar Laraba
- Hakan ya biyo bayan mimbarin gangamin siyasa da suke zaune a kai ya ruguje yayin wani taro da suka hallara a Ijebu-Jesa
- Daga cikin wadanda suke kan mimbarin lokacin da lamarin ya faru akwai mataimakin gwamna, Kola Adewusi da wasu jami'ai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - An shiga fargaba a jihar Osun a ranar Laraba bayan rugujewar mimbarin siyasa da mutane, ciki har da Gwamna Ademola Adeleke, suke kai.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wani gangamin siyasa da aka gudanar a Ijebu-Jesa yayin da ake shirye-shiryen zaben gwamna a Osun.

Source: Twitter
Mimbari ya ruguzo da Gwamnan Osun
Wani bidiyo na dakika 30 da jaridar Punch ta samu wanda ya nuna lokacin da mimbarin ya kife alhali Gwamna Adeleke da mataimakinsa, Kola Adewusi na kan shi
Shugaban majalisar dokokin jiha, Adewale Egbedun, da kakakin kwamitin yakin neman zaben gwamnan, Imole Pelumi Olajengbesi na daga cikin wadanda suke kan mimbarin a lokacin da lamarin ya faru.
An samu tsaiko a taron siyasar
Wata majiya da ke wurin taron, wadda ta nemi a sakaya sunanta domin ba a ba ta izinin yin magana ba, ta ce lamarin ya kawo tsaiko ga gudanar da taron.
Sai dai ta kara da cewa daga baya an ci gaba da taron bayan jami’an tsaro sun fitar da wadanda abin ya shafa daga wajen.
Ta ce:
“Lamarin ya faru. Taron bikin kaddamar da masu yakin neman zaben Imole ne na mazabar tarayya ta Obokun/Oriade. An gudanar da taron a Ijebu-Jesa, kuma taron ya samu halartar jama’a da yawa.
“Gwamnan da wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwarsa suna zaune sai mimbarin ya ruguje. Babu wanda ya rasa ransa. An ci gaba da taron kuma gwamnan ya yi wa jama'a jawabi bayan lamarin,”

Source: Twitter
Bayanin da gwamnatin Osun ta yi
Da aka tuntubi mataimakin kakakin gwamnan jihar, Oladele Bamiji, ya ce lamarin ba shi da tsanani kamar yadda ake yadawa.
“Bayan haka taron ya ci gaba lafiya tare da gwamna da mambobin majalisar zartarwarsa. Babu wanda ya ji rauni.
“Da a ce wani mummunan hatsari ya faru, da ba a ci gaba da taron ba. Babu asarar rai. Bayan gwamnan ya bar wurin taron, ya halarci wani taro a karamar hukumar Odo-Otin,”
In ji Bamiji.
Ga bidiyon da Premium IDAN ya wallafa a X:
Gwamna Adeleke ya tube sarki a Osun
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya tube Joseph Oloyede daga sarautar Apetu na Ipetumodu bayan da aka same shi da laifin damfara a Amurka.
Mai taimaka wa Adeleke kan harkokin yada labarai, Olawale Rasheed, ne ya sanar da tube Oloyede a cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai.
A watan Agustan 2025 aka yanke wa Oloyede hukuncin daurin wata 56 a gidan yari bayan an same shi da laifin damfarar gwamnatin Amurka Dala miliyan 4.2 na COVID-19.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

