'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wurin da Dalibai ke Yin Jarabawar WAEC a Kogi
- 'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare da ke Iluke Bunu a jihar Kogi, suka kashe mutum uku ciki har da mataimakin shugaba
- Rahotanni sun ce maharan sun kuma sace dalibai uku da wasu mazauna yankin yayin harin da suka kai makarantar
- Rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu ba a tabbatar da sace mutane da yawa ba, tana mai cewa an kashe dan bindiga daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - 'Yan bindiga sun kai mummunan hari a makarantar sakandaren gwamnati da ke Iluke Bunu a karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi.
Maharan sun yi sanadin mutuwar mutum uku, ciki har da Mataimakin Shugaban Makaranta, Malam Gani Anifowose.

Source: Original
Daily Trust ta ce rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:45 na safiyar ranar Laraba yayin da dalibai ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC.
'Yan bindiga sun farmaki masu yin WAEC
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa manufar maharan ita ce kai hari kan daliban da ke rubuta jarrabawar WAEC a cibiyar jarrabawar da ke Iluke Bunu.
Wata majiya ta ce:
"'Yan bindigar sun fi mayar da hankali kan dakin jarrabawar WAEC da ke Iluke Bunu. Sun kashe Mataimakin Shugaban Makaranta, Malam Gani Anifowose, tare da wasu mutum biyu sannan suka sace wasu dalibai da mazauna yankin."
Sunayen wadanda aka kashe
Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da harin tare da bayyana sunayen mutanen da suka mutu.
A cewar rundunar, wadanda suka rasa rayukansu sun hada da, Malam Ganiyu Anifowose, mataimakin shugaban makaranta, Mista Sunday Jacob Alhassan mai shekaru 70 da Sunday Ayele mai shekaru shida
Matakin da jami'an tsaro suka dauka
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza, ya ce maharan sun shiga yankin ne a kan kusan babura 40 dauke da makamai.
Da samun rahoton harin, jami'an 'yan sanda daga shiyyar Kabba A tare da rundunar Mopol, jami'an musamman, sojoji da masu yan sa-kai suka garzaya wurin.
Jami'an tsaron sun fafata da maharan a wani mummunan musayar wuta wanda ya tilasta masu tserewa zuwa cikin daji, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Source: Twitter
'Dan bindiga ya mutu yayin artabu
Rundunar 'yan sanda ta ce an kashe dan bindiga guda yayin musayar wutar, yayin da daya daga cikin jami'an tsaro ya samu raunin harbin bindiga kuma yana karbar magani.
Duk da rahotannin da ke cewa an sace dalibai uku da wasu mazauna yankin, rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu babu cikakkiyar hujjar da ke tabbatar da sace mutane da yawa.
An rufe wasu makarantu a jihar Edo
A wani labarin, kun ji cewa wani rahoton sirri da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta fitar ya yi gargaɗin yiwuwar sace ɗalibai da yawa a makarantun jihar Edo.
DSS ta ba da shawarar ƙara tsaro a makarantu tare da haɗa kai da 'yan banga da mafarauta na cikin al'umma domin tabbatar da tsaron dalibai.
Bayan fitowar rahoton, Gwamnatin Edo ta ba da umarnin rufe makarantun sakandare uku a ƙaramar hukumar Akoko-Edo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

