"Iran Ta Fara Sauko Wa," Shugaban Amurka Ya Yi Magana kan Tattaunawar Sulhu da Isra'ila
- Shugaba Donald Trump ya ce watakila ƙasar Amurka ta shiga faɗan Isra'ila da Iran wataƙila kuma ba za ta shiga rigimar ba
- Sai dai Trump, wanda ke da kyakyyawar alaƙa da Isra'ila, ya ce Iran ta nemi a zauna tattaunawa domin kawo ƙarshen wannan yaƙi da ya ɓarke
- Wannan kalamai na Trump na zuwa ne a rana ta shida tun bayan fara musayar wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana duba yiwuwar taimaka wa Isra’ila wajen kai wa kasar Iran hare-hare a yaƙin da ya ɓarke.
Shugaba Trump ya kuma yi ikirarin cewa Tehran ta nemi a zo a zauna tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicinta da Isra'ila.

Asali: Getty Images
Donald Trump ya bayyana haka ne a wurin taron ɗora sabuwar tuta a fadar shugaban Amurka watau White House yau Laraba, kamar yadda BBC News ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Trump ya buƙaci Iran ta miƙa wuya
Trump ya sake maimaita kiran da ya yi wa Iran da ta gaggauta miƙa wuya ba tare da gindaya wani sharaɗi ba, yana mai cewa hakurinsa ya ƙare.
Da aka tambaye shi ko zai shiga yaƙin ya taimakawa kawar Amurka watau Isra'ila, Shugaba Trump ya ce:
"Wataƙila na yi hakan, watakila kuma ba zan yi ba, babu wanda ya san abin da zan yi. Abu ɗaya da zan iya faɗa maku shi ne Iran na cikin matsala, kuma sun nemi a zauna tattaunawa."
Amurka ta yi ikirarin cewa Iran ta nemi sulhu
Trump ya ce Iran ta ce za ta iya turo jami’ai zuwa Fadar White House domin tattaunawa kan shirin nukiliyarta a kokarin dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kai mata, amma ya kara da cewa lokaci ya ƙure.
“Na ce masu lokaci ya kure, watakila mu zauna, amma akwai bambanci tsakanin yau da makon da ya gabata, ko ba haka ba? Babban bambanci.
“Sun ce za su iya zuwa har White House. Wannan dai ya nuna jarumtaka, amma kuma ba abu ne mai sauƙi a gare su ba.”

Asali: Getty Images
Shin za a sulhunta kasar Iran da Isra'ila?
Lokacin da aka tambaye shi ko lokaci ya kure don tattaunawa tsagaita wuta da Iran, shugaban Amurka ya ƙara da cewa ba a makara ba har yanzu.
A baya, Trump ya fi so a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen shirin nukiliyar Iran, inda ya nemi a ƙulla sabuwar yarjejeniya da za ta maye gurbin wadda ya soke a 2018.
Amma tun bayan da Isra’ila ta fara kai hari kan Iran kwanaki shida da suka wuce, Trump ya fara nuna goyon baya ga ƙawar Amurka, rahoton Vanguard.
An yi wa shirin nukiliyar Iran illa
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar IAEA ta tabbatar da cewa Isra'ila ta lalata muhimman cibiyoyi biyu da Iran ke amfani da su a shirin ƙera nukiliya.
Hukumar ta ce duka wannan wurare biyu na karkashin kulawa da tantancewar IAEA ne a baya, bisa tsarin yarjejeniyar JCPOA da aka cimma da Iran
Tun kafin bayanin IAEA, rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sanarwa cewa ta kai samamen sama a yankin Tehran domin ruguza shirin nukiliyar Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng