Jerin Kasashen Duniya da Suka Yi Allah Wadai da Isra'ila saboda kai Hari Iran
A makon da ya wuce kasar Isra'ila ta fara kai hari da makamai masu linzami zuwa Iran wanda hakan ya jawo martani daga wasu kasashen duniya.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - A makon da ya wuce aka fara kazamin fada tsakanin Iran da Isra'ila inda suka rika kai wa juna farmaki da makamai masu linzami.
Kasancewar Isra'ila ce ta fara harba makamai a Iran, wasu da dama daga cikin shugabannin duniya sun yi Allah wadai da matakin.

Asali: Getty Images
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin kasashen da da suka yi Allah wadai da matakin da Isra'ila ta dauka na kai fara kai hari Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Saudiyya ta yi Allah wadai da kai hari Iran
Saudiyya ta yi Allah-wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai wa Iran, inda ta bayyana su a matsayin “zalunci” da “cin zarafi a fili” da ke keta ikon mulkin kai da tsaron Iran.
Legit Hausa ta rahoto cewa kasar Saudiyya ta ce harin ya saba wa dokoki da ka’idojin kasa da kasa.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta yi kira ga al’ummar duniya da kuma Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su dauki alhakin dakatar da harin.

Asali: Twitter
Baya ga Allah wadai da harin, Saudiyya ta yi alkawarin cigaba da kula da alhazan Iran har zuwa lokacin da za su samu damar komawa kasar su.
2. Turkiyya ta soki kai hari a Iran
Majalisar kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan Iran a makon da ya wuce inda ta ce hakan barazana ne ga zaman lafiyan duniya.
Rahoton Middle East Monitor ya ce majalisar ta bayyana cewa Isra’ila na amfani da dabarun tada rikici a yankin, inda take kitsa harin Iran da Gaza a lokaci guda.

Asali: AFP
Majalisar ta kuma bayyana yadda dubban rayuka suka salwanta a Gaza, musamman na mata da yara da ke jiran agaji aka kashe su.
Ta kara da cewa:
“A tsawon shekaru, ba wai mamaya da danniya kadai ba, har da wariyar launin fata da kisan gilla, al’ummar Falasɗinu na fama da yunwa da rashin kulawa daga duniya.”
3. Najeriya ta soki harin Israila a Iran
Gwamnatin Najeriya ta yi tir da harin da Isra'ila ta kai kan Iran a makon da ya wuce tana mai bukatar a tsagaita wuta.
Wani rahoto da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa ofishin harkokin wajen Najeriya ne ya fitar da sanarwa kan lamarin.

Asali: Facebook
A gargagin da Najeriya ta yi, ta bayyana fargabar jawo babban rikici a yankin Gabas ta tsakiya idan lamarin ya cigaba.
4. Rasha ta caccaki Isra'ila saboda harin Iran
Kasar Rasha ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai kan Iran tana mai cewa ya saba dokar kasa da kasa.
Rahoton Reuters ya nuna cewa kasar Rasha ta ce ta hanyar sulhu da tattaunawa ne kawai za a iya shawo kan maganar nukiliya a Iran.

Asali: Getty Images
Rasha ta ce cigaba da kai hare hare da Isra'ila ke yi a Iran baraza ne ga zaman lafiyan duniya ba Gabas ta Tsakiya kadai ba.
5. Kasashe 20 sun soki kai hari a Iran
A wani mataki da suka dauka a dunkule, kasashen Larabawa 20 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai wa Iran.
Sanarwar ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke kara tsananta, wanda ke barazana ga zaman lafiyar yankin.
Arab News ta ce kiran ya fito ne daga kasashen Saudiyya, Masar, Jordan, UAE, Pakistan, Bahrain, Brunei, Turkiyya, Chadi, Aljeriya.
Sauran kasashen sun hada da Comoros, Djibouti, Sudan, Somalia, Iraq, Oman, Qatar, Kuwait, Libiya da Mauritania.

Asali: Getty Images
Makaman Isra'ila sun fado Tel Aviv
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Isra'ila ta yi kuskure wajen harba makamai zuwa Iran a yakin da suke yi.
Rahotanni sun nuna cewa makaman da Isra'ila ta harba sun samu matsala a sararin samaniya, inda suka fado Tel Aviv.
Wani jami'in Amurka da ba a bayyana sunan shi ba ya ce Isra'ila za ta iya fuskantar karancin makaman kare kai idan yakin ya cigaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng