'Suna da Makamai,' A Karshe Trump Ya Ce Iran ba Irin Venezuela ba ce
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana haɗarin da ke tattare da kai hari ta ƙasa kan Iran domin kwace Uranium ɗin da aka tace
- Trump ya yi magana yana mai jaddada cewa suna sa ido da kyamarori masu ƙarfi a kansa a lokacin da ya yi bayani kan Mojtaba Khamenei
- Shugaban Amurka ya nuna cewa shiga Iran ta kasa zai iya haifar da hadari saboda har yanzu suna da sauran makamai masu linzami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - A wata hira da aka yi da shugaban Amurka, Donald Trump a daren Alhamis, ya ce babu wani dalili da zai sa a cire uranium ɗin da aka tace a Iran.
Ya bayyana cewa an rufe sinadarin a cikin wani wurin da ba za a iya isa ba, inda ya ƙara da cewa ba ya son sojojin Amurka su shiga su kwace shi.

Source: Getty Images
Kasar Iran ba Venezuela ba ce
Yayin da yake karin haske kan rashin shiga kasar Iran ta kasa su kwace sanadarin Uranium da ake hada nukliliya da shi, Ynet News ta wallafa cewa Trump ya ce:
“Mun yi tunani a kai, amma ban so mu shiga wani yanayi da za mu tilasta wa kanmu shiga can ba,”
“Ba kamar Venezuela ba ce, inda za ka shiga ka fita cikin mintuna kaɗan mutane suna yi maka bankwana, amma a nan za ka bukaci kayan aiki masu yawa, ka ɗaga su ta sama, kuma kana cikin yankin da ake yaƙi.”
Trump ya kara da cewa:
“Ba ya son ya zama Jimmy Carter,”
Yana nuni da rikicin garkuwa da mutane bayan Juyin Juya Halin Musulunci a Iran.
Game da kwace Uranium a Iran, Trump ya kara da cewa:
“Za ka bukaci zama a can na mako ɗaya ko biyu, kana bukatar manyan kayan aiki, ka shigar da su ta sama, kuma kana cikin yankin yaƙi.
"A farkon lokaci mun yi tunanin yiwuwar yin hakan domin ba za su gano ba nan take, amma daga baya za su gane saboda aikin zai ɗauki lokaci kuma yana bukatar manyan shirye-shirye.
"Don haka za mu iya ɗaukar uranium ɗin, amma na ce ban son hakan.”
Ga bidiyon da Trump ya yi magana da Al Jazeera ta wallafa a X:

Source: Getty Images
Iran na da makamai inji Trump
Shugaban ya ci gaba da bayyana haɗarin aikin tura sojoji ta kasa domin kwace uranium a Iran, inda ya ce har yanzu kasar na da makamai
“Nan da nan Iranawa za su gano inda kuke.
"Har yanzu suna da makamai masu linzami, ma’ana za su iya kai hari sannan su ci gaba da harba su.
"Ban so hakan ba. Za mu iya ɗaukar uranium ɗin yanzu idan muna so, kuma ban tsammanin za su iya hana mu, amma babu wani dalili na yin hakan.”
Trump na son ganawa da Khamenei
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaba Donald Trump ya ce yana sa ran zai gana da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei.
Mojtaba bai fito bainar jama’a ba tun bayan fara yaƙi da Amurka, lokacin da Donald Trump ya hada kai da Isra'ila ya kai wa Iran hari.
Shugaba Trump ya ce har yanzu jagoran na da tasiri a harkokin Iran duk da an ce ya rasa sassa daban-daban na jikinsa a hare-haren.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


