Donald Trump Ya Yi Magana kan Yiwuwar Shiga Faɗan Iran da Isra'ila da Ake Yi

Donald Trump Ya Yi Magana kan Yiwuwar Shiga Faɗan Iran da Isra'ila da Ake Yi

  • Shugaba Donald Trump na Amurka zai yanke hukunci cikin makonni biyu ko kasar za ta shiga yakin Isra'ila da Iran
  • Iran ta fara rajistar gidajen da aka barnata yayin da Minista Farzaneh Sadegh ta ce za su tallafa sosai wajen gyara gidajen da aka lalata
  • Shugaban Hezbollah, Naim Qassem, ya ce kungiyar ba za ta tsaya gefe ba, za ta dauki matakin da ya dace

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Fadar 'White House' ta yi magana kan yiwuwar shiga yakin Iran da Isra'ila da ake cigaba da yi.

Fadar ta ce Shugaban Amurka Donald Trump zai yanke hukunci cikin makonni biyu ko Amurka za ta shiga yakin Isra’ila da Iran.

Akwai yiwuwar Trump ya shiga yakin Iran da Isra'ila
Donald Trump zai yanke shawarar shiga yakin Iran da Isra'ila a mako 2. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Rahoton Al Jazeera ya ce Trump na iya amfani da wa’adin makonni biyu a matsayin dabara don ya boye ainihin shirinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Iran, Isra'ila ke cigaba da gwabzawa

Hakan na zuwa yayin da ake cigaba da kai ruwa rana tsakanin Iran da Isra'ila wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Ministan Tsaron Isra’ila, Katz ya bayyana cewa “kawar da” jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, na daga cikin manufofin yakin kasar.

Majiyoyi sun ce gwamnatin Iran ta fara rajistar gidajen da suka lalace a hare-haren Isra’ila a kasar.

Ministar Raya Birane, Farzaneh Sadegh ta yi alkawarin “cikakken tallafi” wajen sake ginawa da gyaran gidajen da yakin ya shafa.

Hezbollah ta soki Donald Trump

Sakataren Hezbollah Naim Qassem ya fitar da wata doguwar sanarwa yana nuna goyon baya ga Iran a kan hare-haren Isra’ila da barazanar Amurka.

Ya ce furucin Trump na yiwuwar kashe Ayatollah Khamenei wani “hari ne ga al’ummar yankin baki daya.”

Akwai yiwuwar Trump ya shiga yakin Iran da Isra'ila
Ana tunanin nan da mako 2 Trump zai yanke shawara kan fadan Iran da Isra'ila. Hoto: Donald J Trump.
Asali: Getty Images

Lokacin da Trump ka iya dauka kafin harin Iran

Marubuciya, Dorsa Jabbari daga Doha ta ce Donald Trump na iya amfani da wannan lokacin a matsayin dabara don ya bawa diflomasiyya dama.

Ta ce wannan na iya zama tarko,” inda Iran za ta bayyana iyakokinta, kuma Trump ya yi amfani da hakan don daukar mataki.

Jabbari ta kuma yi misali da lokacin da Trump ya bai wa Putin wa’adin makonni biyu kan Ukraine, amma bai dauki mataki ba.

Ya ce:

“Trump na iya kai hari koda gobe, yana amfani da batun wa’adi a matsayin mafaka, kuma yana barin kofar tattaunawa a bude."

Bishara ya ce hakan na iya nufin Trump na bai wa Turawa lokaci domin kowa ya fito da fuska a cikin wannan rikici.

Ali Harb daga Washington ya rawaito cewa mai sharhi Negar Mortazavi ya ce hare-haren Isra’ila na kan jama’ar Iran ba gwamnati kadai ba.

Kamfanin dillancin labarai Tasnim ya ce na’urorin kariya daga hare-haren sama na ci gaba da aiki a gabas, yamma da tsakiyar Tehran.

Ana ƙoƙarin hana Amurka shiga yakin Iran, Isra'ila

Kun ji cewa wasu 'yan majalisar Amurka sun gabatar da kudirin doka domin hana amfani da sojojin Amurka a yaki da Iran ba tare da amincewar su ba.

Kudirin ya samu goyon bayan wasu 'yan majalisa, inda suka ce tsarin mulkin Amurka bai ba shugaban kasa shi kadai damar kaddamar da yaki da wata kasa ba.

Yan majalisun sun jaddada cewa Amurkawa ba sa bukatar sake fadawa cikin wani sabon yaki a Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.