Wata Sabuwa: Hisbah Ta Kafa Sharadin Sakin Matar Auren Gata a Kano

Wata Sabuwa: Hisbah Ta Kafa Sharadin Sakin Matar Auren Gata a Kano

  • Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano ya gargadi ma’auratan da za su shiga shirin auren gata na jihar game da saki ba tare da izini ba
  • Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa ba za a ba su damar yin saki ba tare da sun fara kai rahoto ga Hisbah domin sasanci ba
  • Ya yi wannan gargadin ne yayin wata ziyara da ya kai inda ake gudanar da gwajin lafiya ga masu shirin aure a ranar Laraba, 10 ga Mayun 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya gargadi masu shirin shiga auren gata a jihar game da saki.

Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da cewa babu wanda ya ke da ikon kashe auren da za a daura masu ba tare da sanin Hisbah ba.

Kara karanta wannan

Auren gata: Abin da Hisbah za ta yi wa maza da mata 3,000 a Kano kafin a biya sadaki

Sheikh Aminu Daurawa
Sheikh Aminu Daurawa yayin wani wa'azi. Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara hedikwatar Hukumar Kula da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ɗaya daga cikin wuraren da ake gudanar da gwajin lafiya ga masu shirin aure.

Dokar Hisbah kan saki a Kano

Sheikh Aminu Daurawa ya ce gwamnatin jihar Kano na zuba kuɗi masu yawa a shirin auren gata saboda fatan tana sa ran auren zai daɗe.

A kan haka ya yi gargadi da cewa:

“Ba mu yarda da saki ba. Duk wanda yake son yin saki saboda kowanne dalili dole ne ya zo Hisbah tunda a nan aka ɗaura auren. Muna da kwamitin sasanci wanda zai zauna ya warware matsaloli kafin a yi tunanin rabuwa,”

Malamin ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da shirin auren gata domin taimaka wa marasa galihu da ke fama da matsalar rashin yin aure.

Kara karanta wannan

Iran ta yi wa Trump martani kan neman ganawa da Mojtab Khamenei

A cewarsa:

“Wasu mutane suna sayar da filayensu, babura ko ma su karɓi bashi domin yin aure. Gwamnan cikin jin ƙai ya yanke shawarar ɗaukar nauyin ma’aurata 1,500. Jihar za ta samar da kayan ɗaki, akwatunan aure, tufafi da kayan abinci.
“Kowanne ma’aurata kuma za su samu N200,000 — N100,000 a matsayin sadaki da N100,000 a matsayin jarin kasuwanci — tare da shinkafa, taliya da man girki. Ana kashe sama da Naira miliyan 250,”.
Kayan da aka tanada domin daurin aure a Kano
Yadda aka tanadi gado, katifa da kayan auren gata a Kano. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin shugaban KSACA a Kano

Shugaban hukumar KSACA, Dr Usman Bashir, ya ce gwajin wani bangare ne na dokar gwajin lafiya kafin aure da aka sanya wa hannu a shekarar 2024.

“Mun gwada lafiyar mutane 3,000 domin tabbatar da cewa sun dace da aure a fuskar lafiya. Ma’auratan da suka ci gwajin za a ba su takardun shaida, yayin da waɗanda aka samu matsalolin lafiya kamar rashin dacewar jini za a ba su shawarar kada su ci gaba da aure."

Kara karanta wannan

'Suna da makamai,' A karshe Trump ya ce Iran ba irin Venezuela ba ne

In ji shi.

Turawa sun ziyarci Kano

A wani labarin, kun ji cewa tawaga ta musamman daga Tarayyar Turai da wasu kasashe ta kai wa Sarki Muhammadu Sanusi II ziyara a Kano.

Tawagar ta hada da jakadan Tarayyar Turai a Najeriya da wakilai daga kasashen Spain, Italy, Faransa da wasu yankunan da ke Turai.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi masu hawa na musamman domin kayatar da su da nuna masu al'adun da jihar Kano ke raya wa tsawon shekaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng