Babu Hutu: Kasar Iran Ta Kai Hare Hare Zagaye na 15 kan Manyan Birane 2 a Israila

Babu Hutu: Kasar Iran Ta Kai Hare Hare Zagaye na 15 kan Manyan Birane 2 a Israila

  • Dakarun rundunar sojin IRGC na Iran sun tabbatar da kai hare-hare zagaye na 15 kan manyan birane biyu na ƙasar Isra'ila
  • Rundunar sojin ta kuma gargaɗi Isra'ila cewa za ta ƙara kaimi wajen kai mata hare-hare musamman a muhimman wurare
  • Wannan sanarwa da sojojin Iran na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan hukumomin Isra'ila sun yi ikikarin cewa Iran ta kai hari asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Dakarun Juyin Juya Hali na Ƙasar Iran wato IRGC sun sanar da kaddamar da wani sabon zagaye na hare-hare da suka haɗa da makaman roka da jiragen yaki marasa matuki a kan Isra’ila.

Wannan sanarwar ta fito ne ta bakin kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran a yau Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025.

Iran ta kai hare-hare zagaye na 15.
Iran ta ƙaddamar da hare hare zagaye na 15 kan birane 2 a Isra'ila Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Aljazeera ta rahoto cewa dakarun sojin Iran sun ce wannan shi ne zagaye na 15 a jerin hare-haren da suke kai wa Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane wurare Iran ta harbawa makamai a Isra'ila?

A cewar IRGC, sabon harin da suka fara ya mayar da hankali ne kan sansanonin sojoji da cibiyoyin masana’antun kayan yaki a manyan biranen Haifa da Tel Aviv, wasu daga cikin mahimman biranen Isra’ila.

Rundunar IRGC ta ce an ƙaddamar da hare-haren ne cikin tsari da haɗin gwiwa, inda aka yi amfani da rokoki da kuma jiragen yaki marasa matuki don kai hari kan mahimmancin wuraren tsaron Isra'ila.

IRGC ta kara da cewa tana ci gaba da amfani da jirage marasa matuƙa da masu yaƙi da kansu kuma su fashe wajen kai farmaki cibiyoyin kariyar Isra'ila da ke Haifa da atel Aviv.

Sojojin Iran sun ƙara gargaɗin Isra'ila

Haka nan kuma rundunar sojin Iran ta gargaɗi gwamnatin Isra'ila, tana mai cewa:

“Za mu ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare da makaman roka a kan duk wata cibiyar soja ko masana’antar da ke da alaƙa da harkokin soji a faɗin Isra’ila. Harin ba zai tsaya nan ba."

Wannan lamari na zuwa ne bayan hukumomin Isra'ila sun yi ikirarin cewa Iran ta kai farmaki wani asibiti a Beersheba, kuma ta jikkata mutane da dama.

Hukumar asibitin ta ce gobara ta hallaka wasu sassa, ta fasa tagogi da rushe rufin gine-gine, wani sashe na asibitin ya lalace matuka, rahoton BBC News.

Ayatollah Ali Khamenei Da Benjamin Natanyahu.
Sojojin Iran sun sanar da kai hare-hare biranen Haifa da Tel Aviv Hoto: Getty Images
Asali: Twitter

Isra'ila ta yi shiru kan sababbin hare-haren Iran

A halin yanzu, babu cikakken bayani daga hukumomin Isra’ila kan irin barnar da harin da Iran ta ce ta kai zagaye na 15.

Sababbin hare-haren da IRGC ta kaddamar ya nuna cewa tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila na ƙara kamari.

Isra'ila ta yi barazanar kashe jagoran Iran

A wani labarin, kun ji cewa Isra'ila ta yi barazana ganin bayan jagoran addinin musulunci na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ne ya yi wannan barazana bayan harin da aka ce Iran ta kai kan wani asibiti a birnin Beersheba.

Ministan ya zargi Ayatollah Khamenei da kasancewa mutum da ke da burin rusa Isra’ila gaba ɗaya ta hannun wakilansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262