Isra'ila Ta Tura Jiragen Yaki, Sun Tarwatsa Sabuwar Cibiyar Hada Nukiliya a Iran

Isra'ila Ta Tura Jiragen Yaki, Sun Tarwatsa Sabuwar Cibiyar Hada Nukiliya a Iran

  • Jiragen Isra’ila sun kai hari a Arak domin dakile shirye-shiryen Iran na hada makaman nukiliya da ake zargin ta ke ci gaba da yi
  • Hukumar kula da nukiliya ta duniya (IAEA) ta tabbatar da harin amma ta ce babu wani abu mai kama da hada nukiliya da ake yi a Arak
  • Yayin da take martani, Iran ta ce harin na Isra'ila bai yi wata barna a cibiyar ta Arak ba, wacce ke da tazarar kilomita 250 daga Tehran

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - Jiragen saman Isra'ila sun kai hari kan wani sabuwar cibiyar sarrafa nukiliya da ake ginawa a tsakiyar Iran, a yayin jerin hare-haren sama.

Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari ne kan cibiyar Arak domin hana amfani da ita wajen "ci gaba da hada makaman nukiliya da Iran take yi."

Isra'ila ta ce ta tura jiragen yakinta, inda suka tarwatsa wata cibiyar hada nukiliyan Iran
Wasu daga cikin jiragen yakin kasar Isra'ila da ke gudu a sararin samaniya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) ta tabbatar da cewa an kai wa cibiyar hari kuma babu wani abu mai alaƙa da nukiliya a cikinta, inji rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce man da aka riga aka yi amfani da shi a cibiyar yana ɗauke da sinadarin plutonium wanda ya ke tarwatsewa kamar nukiliya idan aka farmake shi.

Binciken IAEA kan cibiyar nukiliyar Arak

Hukumar IAEA ta ce Iran ta cire wata na'ura ta 'calandria' daga cibiyar Arak, kuma ta sanya ya koma "marar amfani," duk a kokarin kin hada nukiliya a cibiyar.

Rahoton hukumar IAEA na ƙarshen Mayu ya ce ana ci gaba da aikin gine-gine kaɗan a cibiyar, kuma Iran tana sa ran za a fara amfani da ita a wannan shekara.

Sai dai, sojojin Isra'ila sun ce gwamnatin Iran da jan kafa wajen kammala wannan sake fasali, inda ta ce hakan yaudara ne, kuma Iran ba ta son daina hada makaman nukiliya a ciki.

Sojojin sun ƙara da cewa:

"Mun kai hari ne kan wani ɓangare da Iran ta yi niyyar amfani da shi don samar da plutonium, wanda zai ba ta damar sake dawo wa da ci gaba da hada makaman nukiliya."

Iran ta yi martani da Isra'ila ta farmaki Arak

Hotunan harin da sojojin suka fitar sun nuna alamar bam yana sauka kan rufin ginin Arak, kuma an ga bangarori da dama na cibiyar na fashewa.

Iran ta ce babu wata barna da harin Isra'ila ya yi kan cibiyar Arak
Cibiyar Arak, inda jiragen yakin Isra'ila suka farmaka a ranar Alhamis, 19 ga Yuni, 2025. Hoto: Maxar / Contributor
Asali: Getty Images

An rahoto cewa Arak, ta na a bangaren Kudu maso Yamma da Tehran, da tazarar tafiyar kilomita 250 (mil 155), kuma ana kiranta da Khondab.

Wani bidiyo da gidan talabijin din Iran ya watsa ya nuna hayaƙi ya turnuke sararin samaniya daga wurin. Haka kuma ya ambato jami'an Iran suna cewa "babu wata barna da harin ya yi."

Gargadin Iran ga Amurka kan taimakawa Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya fara duba yiwuwar tallafa wa Isra’ila wajen kai farmaki kan cibiyoyin nukiliyar Iran, yayin da ya yi barazana ga Ali Khamenei.

Amma Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani, tana mai cewa wannan ba yaƙin Amurka ba ne, don haka bai dace Trump ya ce zai shiga ba.

Iran ta yi gargadi mai zafi cewa duk wani yunkurin taimako daga Amurka ga Isra’ila zai janyo mummunar rikici da zai mamaye dukkanin kasashen Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.