Rai Ya Baci: Gwamna zai Kori Hadiman shi da Suka Ki Shiga APC cikin Sa'o'i 48

Rai Ya Baci: Gwamna zai Kori Hadiman shi da Suka Ki Shiga APC cikin Sa'o'i 48

  • Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya gargadi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ba sa goyon bayan jam'iyyar APC
  • Ya bukaci waɗanda ba su APC ko suka fito fili suka nuna biyayya ga wasu jam’iyyun siyasa da su yi murabus daga muƙamansu nan take ko ya kore su
  • A cewar gwamnan, an bai wa waɗanda abin ya shafa wa’adin sa’o’i 48 su miƙa takardun murabus dinsu ga ofishin sakataren gwamnatin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasa da suka ƙi komawa jam’iyyar APC da su yi murabus ko kuma a kore su.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Fintiri ya koma APC daga jam'iyyar adawa ta PDP kuma ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2027.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri
Gwamnan Adamawa a wajen wani taro yana jawabi. Hoto: Adamawa State Government
Source: Twitter

Umarnin Fintiri ga hadimansa

Punch ta wallafa cewa Fintiri ya gargadi hadiman shi ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun jami'in yaɗa labarai na gwamnan, Humwashi Wonosikou.

Wonosikou ya ce:

“Ana umartar duk masu riƙe da muƙaman siyasa a wannan gwamnati waɗanda suka fito fili suka nuna biyayya ko suka koma wasu jam’iyyun siyasa da su yi murabus daga muƙamansu nan take.
“Wannan umarni ya zama dole domin kare biyayya ga gwamnati, ladabtarwa da mutuncin aikin gwamnati.”

Gwamnan ya ce ana sa ran masu riƙe da muƙaman siyasa za su goyi bayan manufofi, shirye-shirye da alkiblar siyasar gwamnatin da suke yi wa aiki.

“Ci gaba da aiki da mutanen da suka koma wata jam’iyya na haifar da babbar barazanar zagon ƙasa, fitar da bayanai da kuma hana aiwatar da manufofin gwamnati da dabarun jam’iyya.
"Saboda haka, ana umartar duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa takardun murabus dinsu ga ofishin sakataren gwamnatin jihar cikin sa’o’i 48 daga lokacin da aka bayar da wannan umarni."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fusata kan rashin tsaro, ya ragargaji Tinubu

“Rashin bin wannan umarni cikin wa’adin da aka kayyade zai haifar da kora nan take daga aiki, dakatar da duk albashi, hakkoki da alawus-alawus, tare da ɗaukar ƙarin matakan hukunci na gudanarwa."
Taswirar jihar Adamawa
Taswirar jihar Adamawa a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Me ya sa Fintiri ya yi umarnin?

An ce umarnin gwamnan ba ya rasa nasaba da ƙin bin sa da yawancin masu riƙe da muƙaman siyasarsa suka yi wajen komawa APC, inda suka ci gaba da kasancewa a jam’iyyar PDP.

Businesss Day ta wallafa cewa umarni ya zo ne a daidai lokacin da wasu daga cikin masu riƙe da muƙaman siyasar suka koma wasu jam’iyyun siyasa a jihar domin yin aiki da nufin kawo cikas ga APC.

'Yan APC sun yi zanga-zanga a Legas

A wani labarin, kun ji cewa daruruwan 'yan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zanga a sakatariyar jam’iyyar ta jihar Legas da ke Ikeja.

Sun yi haka ne suna neman a sake duba sakamakon zaɓen fitar da gwani na kujerun majalisar wakilai da majalisar dokokin jihar Legas a wasu mazaɓu bisa zargin samun kura-kurai.

Rahoto ya nuna cewa masu zanga-zangar sun fito daga mazaɓu da suka haɗa da Amuwo-Odofin, Amuwo-Odofin II, Ajeromi-Ifelodun da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng