Ba a Gama Makokin Mutuwar Ebrahim Raisi ba, an Tafka Girgizar Kasa a Iran

Ba a Gama Makokin Mutuwar Ebrahim Raisi ba, an Tafka Girgizar Kasa a Iran

  • An samu girgizar kasa mai karfin awo 3.7 ta afku a Malayer da ke lardin Hamedan a yammacin kasar Iran a ranar Litinin
  • Girgizar kasar ta afku a nisan kilomita tara daga Samen, kilomita 18 daga Melayer, da kuma kilomita 18 daga Oshtorinan
  • Wannan girgizar kasar na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Raisi ya mutu a wani hatsarin jirgin sama a jiya Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kasar Iran - Rahotanni sun bayyana cewa girgizar kasa mai karfin awo 3.7 ta afku a Malayer da ke lardin Hamedan a yammacin kasar Iran a ranar Litinin.

An tafka girgizar kasa a Iran
Ana makomin mutuwar Ebrahim Raisi, an yi girgizar kasa a Iran. Hoto: Radiokukka
Asali: Getty Images

Girgizar kasa ta afku a yammacin Iran

A cewar cibiyar nazarin yanayin kasa da ke a jami'ar Tehran, girgizar kasar ta afku da misalin karfe 08:20:52 agogon kasar, kuma tana da zurfin kilomita 10.

Kara karanta wannan

Wanene Mohammad Mokhber, shugaban rikon kwaryan kasar Iran? Abin da muka sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Girgizar kasar ta afku a nisan kilomita tara daga Samen, kilomita 18 daga Melayer, da kuma kilomita 18 daga Oshtorinan, in ji rahoton IRNA.

An mutu a sanadiyyar girgizar kasar Iran?

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kawo yanzu dai ba a samu asarar rayuka ko jikkata ba.

Lamarin girgizar kasar na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Raisi ya mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, lamarin da ya jefa kasar cikin makoki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Ali Khamenei, ya ayyana zaman makoki na kwanaki 5 domin girmama marigayi shugaban kasar da tawagarsa.

Iran: Jirgin Ebrahim Raisi ya yi hatsari

Mun ruwaito wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da wasu manyan jami'ai ya yi hatsari a yammacin kasar.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Shugaba Raisi yana dawowa ne daga bikin bude madatsar ruwa a kan iyakar kasar Iran da Azarbaijan lokacin da jirginsa ya yi hadari a yankin Varzaqan ranar Lahadi.

Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian, da gwamnan lardin Azarbaijan ta gabas Malek Rahmati, da babban limamin Tabriz, Hojjatoleslam Al Hashem da wasu da dama na cikin jirgin.

Shugaban Iran ya rasu a hatsari jirgi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi ya mutu a hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi tare da wasu mukarrabansu a jiya Lahadi.

Masu aikin ceto sun bayyana cewa babu wanda ya rayu a cikin mutane takwas da ke kan jirgin yayin da kuma aka kwaso gawarwakin su zuwa babban birnin kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.