'Kokarin da Janar Abdulsalami Abubakar Ya Yi kan Abiola kafin Rasuwarsa'
- Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Janar Abdulsalami Abubakar ya yi ƙoƙarin ganin an saki MKO Abiola kafin rasuwarsa
- Obasanjo ya ce Abdulsalami ya taka muhimmiyar rawa bayan mutuwar Janar Sani Abacha, inda ya saki fursunoni, sannan ya dawo da dimokuraɗiyya
- Goodluck Jonathan da sauran manyan baki sun yaba wa Abdulsalami bisa jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da miƙa mulki cikin lumana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana rawar da Abdulsalami Abubakar ya taka game da lamarin MKO Abiola.
Obasanjo ya ce tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi ƙoƙarin ganin an saki marigayi Mashood Abiola kafin rasuwarsa.

Source: Getty Images
Obasanjo ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da littattafai uku da aka wallafa domin girmama cikar Abdulsalami shekaru 84 a duniya, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi maganar mutuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan Bindiga
Obasanjo ya tuna kyawawan halayen Abdulsalam
Ya bayyana Abdulsalami a matsayin babban jagoran soja, jajirtaccen jami'i, ɗan kishin ƙasa, mai kishin Najeriya da kuma mai sasanta rikice-rikice.
Obasanjo ya ce Abdulsalami ya gudanar da al'amura cikin hikima bayan mutuwar Janar Sani Abacha, lokacin da ƙasar ke cikin ruɗani da rashin tabbas.
A cewarsa, Abdulsalami ya fara sakin fursunonin siyasa, ciki har da shi kansa Obasanjo, sannan ya ɗauki matakai domin ganin an saki MKO Abiola da yake tsare.
Ya ce:
"Kamar yadda shugaban majalisar dattawa ya bayyana, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amfana daga wannan. Mataki na gaba shi ne yadda za a saki MKO Abiola, kuma kana ci gaba da sanar da ni duk abin da ke faruwa tare da isar da saƙonni ga iyalansa."
Obasanjo ya ƙara da cewa, ɗan MKO Abiola mai suna Kola ya riga ya isa Abuja domin ɗaukar mahaifinsa lokacin da abin da ba a yi tsammani ba ya faru.

Kara karanta wannan
2027: Tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya gana da jagororin tafiyar Obi da Kwankwaso
Tsohon shugaban ƙasar ya yaba wa Abdulsalami Abubakar saboda rawar da ya taka wajen kafawa da kuma ɗorewar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Source: UGC
Jonathan ya yabawa Abdulsalam Abubakar
A nasa jawabin, tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana Abdulsalami a matsayin fitaccen dattijo mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa bil'adama hidima.
Jonathan ya tuna irin gudunmawar da Abdulsalami ya bayar wajen jagorantar Najeriya zuwa miƙa mulki cikin lumana zuwa tsarin dimokuraɗiyya, cewar TheCable.
Ya yaba masa saboda jarumtaka da rashin son kai wajen inganta zaman lafiya da ci gaban ƙasa, yana mai cewa ana auna gadon mutum da irin nasarorin da ya bari.
Jonathan ya kuma ce Abdulsalami ya taimaka wajen tabbatar da daidaiton dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da ƙin amincewa da matsin lamba na ci gaba da zama a mulki fiye da lokacin da ya kamata.
Abdulsalami ya fadi dalilin mutuwar Abiola
An ji cewa Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya kawo wasu karin bayanai game da mutuwar MKO Abiola a Najeriya.
Abdulsalam ya ce ba a ba tawagar Amurka damar ganin Abiola ba da farko, amma ya ba da umarnin a kai su wajensa.
Ya bayyana cewa Abiola ya fara tari da zufa yayin ganawa da tawagar kafin daga bisani ya rasu, lamarin da ya girgiza kasar.
Asali: Legit.ng
